Allah yayi wa Sarkin Gaya, Ibrahim Abdulkadir Rasuwa

A safiyar Laraba ne Allah yayi wa sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir dake jihar Kano rasuwa.
Daya daga cikin hadiman gwamnan Kano Ibrahim Abubakr ya bayyana rasuwar maimartaba marigayi sarki Ibrahim a shafin Facebook din sa.
Ibrahim ya bayyana cewa mai martaba sarkin gaya ya rasu ne a bayan fama da yayi da gajeruwar rashin lafiya.