Kuskure ne ƙananan hukumomi su riƙa dogaro da kuɗin Gwamnatin Tarayya- Ɗan Majalisa

Ismat Suleja

Shugaban kwamitin kula da raya ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya a Majalisar Dokokin Jihar Neja, Hon. Shuaibu Liman Iya, ya bayyana cewa; ko kaɗan babu dabara ga ƙaramar hukuma ta zama mai dogaro ne ga kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke turo mata a duk wata.
A tattaunawarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman su a zauren Majalisa, Hon. Liman Iya ya ce; wajibi ne ga ƙananan hukumomi su mayar da hankali wurin zaƙulo hanyoyin bunƙasa kuɗaɗen shiga a ƙaramar hukumar su ta yadda za su rinƙa dogaro da kan su da kuma rage yawan dogaro da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke turo masu, wanda bayan an cire wasu kuɗaɗe da doka ta tabbatar da su ƙananan hukumomin kan shiga garari ta yadda wasu ma kan kasa biyan albashin ma’akatan su balle har a samu a yi wa jama’a aikin raya ƙasa.
Ɗan Majalisar mai wakiltar mazabar Suleja ya tabbatar da cewa; tuni Majalisar ta kammala shirye- shiryen rangadin gani da ido da ziyarar ƙananan hukumomi domin tabbatar da ganin sun aiwatar da aiyukan da ake ba su kuɗaɗe a kai. Ya ce za su fara wannan ziyarar da ake ƙira da “oversights function” a sati mai zuwa

Kuskure ne ƙananan hukumomi su riƙa dogaro da kuɗin Gwamnatin Tarayya- Ɗan Majalisa
Ku daina la’antar shugabanni saboda wahalar rayuwa, Sanusi ga ƴan Najeriya

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 22, 2021 11:28 AM