Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗaliban makarantar Sakandare da aka sace a Zamfara sun kubuta

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da kubutar da ɗaliban makarantar saƙandaren Ƙaya dake ƙaramar hukumar Maradun da ƴan bindiga suka sace a kwanakin baya.

Rahotanni daga gidan gwamnatin jihar sun ce gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun kubutar da dukkan ɗaliban tare da malaman su.

Tuni aka gabatar da ɗaliban da malaman su a gidan gwamnati inda suka gana da gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle.

Ƙarin bayani na tafe….

An wallafa wannan Labari September 12, 2021 10:09 PM