Najeriya na bukatar sama da naira biliyan 600 don dakile yaduwar Korona a kasar

Farfesa a fannin koyar da kiwon lafiya a jami’ar jihar Legas Akin Osibogun ya bayyana cewa Najeriya na bukatar naira biliyan 693 domin dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Osibogun ya fadi haka ne a taron masu gudanar da bincike da aka yi a jami’ar jihar Legas a cikin makon jiya.

Taken taron shine ‘Tsaro hanyoyin kawar da cutar korona’ sannan shi Osibogun ya yi jawabi akan ‘Rigakafi ya fi magani: Darasin da aka koya daga annobar korona’

Ya ce za a kashe akalla naira biliyan 693 domin yi wa mutum miliyan 140 allurar rigakafin korona da ruwan maganin AstraZeneca daga cikin mutum miliyan 206 ‘yan Najeriya.

“Yin allurar rigakafin korona da ruwan maganin AstraZeneca sau biyu ake yi sannan siyan yawan da zai isa a yi wa mutum miliyn 140 zai ci Dala miliyan 840 da kudin biyan ma’aikatan da za su rika yi wa mutane allurar rigakafi Dala miliyan 840 jimalaya tashi a Dala biliyan 1.680.

“Mun yi wannan lissafi bisa ga yadda farashin Dala daya yake yanzu akan naira 412.

Allurar rigakafin cutar korona a Najeriya

Idan ba a manta ba a ranar 5 ga Maris 2021 ne gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona a kasar nan.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce gwamnati na burin ganin anyi wa akalla mutum kashi 70% allurar rigakafin.

Gwamnati ta ce za ta yi wa kashi 40% rigakafin a shekarar 2021 sannan ta kammala Kashi 30% a shekarar 2022.