Dalilai 10 da suka sa ba za a iya yin hannun riga da Korona ba sai dai a hakura da zaman ta kawai – Manazarcin Kwayoyin Cututtuka

Dalilai 10 da su sa ba za a iya yin hannun riga da Korona ba sai dai a hakura da ita – Manazarcin Kwayoyin Cututtuka
Wani masanin ilimin kwayoyin cutar ‘Virus’ kuma malamin koyar da darasin ‘Microbiology da Molecular genetics’ a jami’ar American University of Nigeria AUN dake Yola jihar Adamawa Malachy Okeke ya ambato wasu dalilai da ya ce sune za su sa a yi wahalar dakile yaduwar Korona a duniya.
A wata takarda da ya rubuta mai taken ‘Kawar da cutar korona ba abune mai yiwuwa ba sai da ko a mafarki’ Za a iya rage yaduwar cutar amma cutar ta zo ta zo amna dirshan ne.
Okeke ya ce korona ba kamar cutar Kyanda bane da aka yi nasarar kawar da shi a shekarar 1970s domin sakamakon bincike da aka gudanar ya nuna cewa korona ba cutar da za a iya kawar dashi bane cikin kankanin lokaci.
Ya ce fahimtar haka zai taimaka wa mutane wajen tsara hanyoyin da za su ci gaba da rayuwa ba tare da cutar ta na tsorata su ba ko kuma kashe su.
Ya ce wanene ke da tabbacin cewa a dalilin matakan da aka dauka domin dakile yaduwar cutar mutane za su iya ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba yi a baya tare da amfani da takunkumin fuska ba, bada tazara tsakin mutane da yin allurar rigakafi ba. Babu wanda ke da wannan tabbaci.
1. Shi dai maganin rigakafin Korona ba warkar da mutane yake yi ba kuma ba ya bada kariyar kamuwa da ita Koronar dole kuma dai kaci gaba da tottoshe hanci da baki.
2. Burin dakile yaduwar cutar ta hanyar yi wa akalla mutum biliyan 7 allurar rigakafin a duniya ba zai yiwu ba saboda yadda wasu kasashen da suka ci gaba ke boye maganin rigakafin domin hana kasashe masu tasowa samun maganin.
3. A lokacin da masana kimiyan suka hada maganin rigakafin babu sakamakon binciken da ya nuna cewa maganin rigakafin na hana mutum kamuwa da cutar duk da cewa an tabbatar da ingancin maganin a jikin mutum.
4. A dalilin haka wadanda aka yi wa rigakafin za su iya kara kamuwa da cutar sannan su yada wa sauran mutane idan ba sun ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar bane.
5. Masana ilimin allurar rigakafi sun ce kariyar da maganin rigakafin korona ke samar wa jikin mutum na dan wani lokaci, sannan sakamakon bincike ya nuna cewa kariyar da maganin rigakafi ke samar wa jikin mutum kan fara raguwa bayan watanni shida.
6. Kariya daga kamuwa da cutar dake cikin maganin rigakafin da aka hada ‘messenger RNA platform’ kamar Pfizer da Modena sun fi saurin raguwa fiye da wanda aka hada da ‘virus-vector platform’ kamar AstraZeneca, Johnson &Johnson.
7. Rashin hana mutum Kara kamuwa da cutar na cikin dalilin da ya sa cutar ta sake barkewa a kasashen USA, Israel, Daular larabawa da wasu kasashen duniya.
8. Cutar korona cuta ce dake canja yanayin akai akai da hakan ya sa WHO ta gano wasu nau’ukan cutar da suka hada da ‘SARS-CoV-2’, Alpha, Beta, Gamma, Delta, Eta, Lota, Kappa da Lambda.
Har yanzu masana kimiya na gudanar da bincike domin gano wasu nau’ukan cutar da za su bullo.
9. Banda mutum dabobbi ma yanzu suna kamuwa da Korona, kamar su mage, kare, jemage na kamuwa da korona.
Har yanzu babu tabbacin mutum na iya kamuwa da cutar daga jikin dabba amma sakamakon bincike ya nuna cewa dabobbi na iya kamuwa da cutar daga jikin mutum.
Mafita
Okeke ya ce daya daga cikin dalilan da ya sa cutar ta ci gaba da yaduwa shine yadda aka yi watsi da kiyaye dokokin cutar.
Okeke ya yi kira ga kasashen duniya da su dawo da wadannan dokoki domin dakile yaduwar cutar.
“Kasashe kamar Israel, Netherlands, Singapore, South Korea, Australia, na cikin kasashen da suka daina amfani da dokar guje wa kamuwa da cutar.
“A dalilin haka cutar ta sake barkewa inda dole kasashen suka nemi wasu makatan da za su dauka domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
“Darasin da ya kamata a dauka a nan shine duk da cewa akwai maganin rigakafin korona kamata yayi a ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin samun kariya.