Buhari ya yi alƙawarin kammala wasu muhimman aiyuka biyu kafin ya sauƙa

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kammala gadar Neja ta biyu mai tsawon kilomita 11.9 da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 120.
Shugaban ya kuma ba da tabbacin cewa za a kammala muhimman ayyuka a karkashin Asusun Raya Ababen more rayuwa na Shugaban kasa (PIDF) kafin mika mulki.

Buhari ya yi alƙawarin kammala wasu muhimman aiyuka biyu kafin ya sauƙa
Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Taraba, Aku Uka, ya mutu

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin buɗe wani taron bita na kwanaki biyu na Ministoci wanda ke gudana a babban ɗakin taro da ke Fadar Shugaban ƙasa a Abuja don tantance matakin cimma muhimman abubuwa 9 da gwamnatinsa ta sa a gaba.
Shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa kan yadda ministocin suka yi aikin da aka ba su cikin shekaru biyun da suka gabata na gabatar da rahotanni ga Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), rahotannin a cewar shugaban suna magana kan abubuwan da gwamnatinsa ta cimma.
Ya lissafa nasarori a fannonin ababen more rayuwa, sufuri, tattalin arziƙi, samar da wutar lantarki, masana’antar man fetur, da sauran su.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari October 12, 2021 5:52 AM