Ganduje ya kori Mu’azu Magaji daga sabon muƙaminsa bisa rashin iya aiki da biyayya

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kori Mu’azu Magaji a matsayin shugaban Kwamitin aikin shimfiɗa Bututun Isar Gas na NNPC/AKK a matsayin wakilin jihar Kano a aikin.

Idan baku manta ba, a watan Afrilun 2020, Ganduje ya kori Magaji a matsayin kwamishinan Ayyuka na jihar Kano saboda murnar rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Malam Abba Kyari.

Daga baya aka sake naɗa shi a matsayin shugaban kwamitin AKK, Daily Nigerian ta ruwaito.

  • Ganduje ya kori Mu’azu Magaji daga sabon muƙaminsa bisa rashin iya aiki da biyayya
  • Buhari ya yi alƙawarin kammala wasu muhimman aiyuka biyu kafin ya sauƙa

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun Kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Garba, a yammacin ranar Litinin ta ce an sanar da cire shi ne saboda rashin iya yin aikin da kuma rashin biyayya.

Kwamishinan ya ƙara da cewa an naɗa Ijiniya Magaji a watan Afirilu, don jagorantar kwamitin tare da fatan zai yi aiki tuƙuru don sa ido kan yadda ake aiwatar da aikin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya kasa zama a hukumar wajen aiwatar da nauyin da aka ɗora masa na sa ido kan aikin wanda gwamnati ke da buri akai.

A cewar sanarwar, jagorancin kwamitin, wanda ya haɗa da wasu abubuwa da dama, tare da haɗin gwiwa da NNPC kan aiwatar da aikin cikin ƙan-ƙanin lokaci bai ɗauki saitin da za a cimma burin da ake so ba.

Sanarwar ta umarci korarren shugaban da ya miƙa lamuran kwamitin ga mataimakin sa, Aminu Babba Ɗan-Agundi.
Gwamna Ganduje ya gode masa kan hidimar da ya yi tare da yi masa fatan samun nasara a kokarinsa na gaba.

An wallafa wannan Labari October 12, 2021 6:22 AM