Ministan shari’a ya ja kunnen alƙalai game da cefanar da shari’a

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya gargaɗi alƙalai game da mutunta dokokin shari’a da kotu da gujewa mayar da shari’a abin ciniki ko wata haja da wanda ya fi kuɗi zai kwashi garaɓasa.
Malami ya yi wannan gargaɗin ne a taron shekarar shari’a ta 2021 da aka gudanar a kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja.

Ministan shari’a ya ja kunnen alƙalai game da cefanar da shari’a
An sace miliyan N345m na magada a asusun kotun Shari’ar musulunci a Kano

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labaran ofishin Ministan ya fitar, Dr Umar Jubrilu Gwandu.
Malami ya ja hankalin alƙalai kan tabbatar da adalci da kare martabar aikinsu wajen aiwatar da hukunci da kuma bai wa al’umma ƙwarin-gwiwar aminta da ɓangaren shari’a.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 14, 2021 1:18 PM