BINCIKEN ‘Pandora Papers’: EFCC ta gayyaci Peter Obi ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi

Hukumar EFCC ƙarƙashin Abdulrasheed Bawa ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Anambra, kuma tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2019, Peter Obi ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.

Wannan shine karon farko da hukumomin bincike na gwamnati musamman EFCC za ta gayyaci wani daga cikin waɗanda binciken ‘Pandora Papers’ ya bankaɗo harkallarsu ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin bincike harda EFCC su taso keyar duk wanda binciken Pandora Papers ya tona asirinsa.

A takardar sammacin da EFCC ta aika wa Obi wanda PREMIUM TIMES ta gani, zai bayyana a hukumar domin fuskartar jami’ai ranar 27 ga Oktoba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Peter Obi ya wafci kuɗaɗen talakawan jigar Anambra ya nausa da su kasashen waje can inda ba zai rika biyan haraji ba ya kafa kamfanoni.

Da aka tambaye shi me ya sa yayi haka sai ya ce bai san ashe idan akwai kamfani wanda ya haɗa hannu da iyalan sa suka kafa suma sai ya bayyana su a fom ɗin bayyana kadarori ɗallaɗalla a lokaci da zai fito takara ba.

Bayan ko wasu kamfanonin na sa da ke kasashen waje ya ci gaba da zama ɗaya daga cikin darektocin su har lokacin da ya zama gwamnan Anambra.

Ita hukumar tara haraji ta ƙasa ta ce ita ma za ta bi duk wanda ya kauce wa biyan haraji da binciken ya fallasa, sai ya dawo ya biya duka harajin da ake bin sa.

Daga baya kuma bayan an buga labarin harƙallar sai ya karyata labarin cewa bita da kulli ake masa, bai aikata laifi ba.

Waɗanda binciken Pandora Papers ya ɓankano harkallar su sun hada da Gwamnonin Osun Gboyega Oyetola da na Kebbi, Abubakar Bagudu da Dapo Abiodun na Ogin, sai kuma sanata Stella Oduah, shugaban NPA, Bello Koko, tsohon gwamnan Kano Kanal Sani Bello da Sambo Dasuki.