Kwankwaso ya magantu game da labarin kwanarsa a hannun EFCC

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi magana game da labarin da wasu manyan Jaridun Najeriya suka wallafa kan cewa hukumar EFCC dake yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama shi har ma ya kwana a hannunta.

Tsohon Gwamnan jihar Kanon wanda hotunan sa suka bayyana a safiyar Lahadi a babban filin jirgin sama na Abuja zai tafi ta’aziyya jihar Ogun kamar yanda shafinsa ya wallafa, Daily Nigerian ta ruwaito ya ce shi da kansa ya kai kansa ofishin EFCC ranar Asabar kuma bai bata lokaci ba ya fice daga hukumar. Ya ce ya je ne domin ya wanke kansa daga zargin karkatar da naira biliyan goma kuɗin ƴan fansho kamar yadda ake tuhumarsa.

Kwankwaso ya kuma ƙaryata cewa bai kwana a ofishin hukumar ba, ya ce bayan ya kammala ganawa da wasu ma’aikatan hukumar na ɗan wasu awanni ya fice daga hukumar.
Jaridun Premium Times da Daily Trust sun tabbatar da labarin ganin Kwankwaso a hukumar EFCC a ranar Asabar, inda a jaridar Daily Trust da ta fita kasuwa ranar Lahadi, Jaridar ta wallafa cewa bisa bincike da ta gudanar Kwankwaso ya kwana a hannun hukumar EFCC.

Tura Wa Abokai

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaDa Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Bungudu ya kubuta daga hannun ƴan bindiga

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.