Gudun kada a kama shi, Kwankwaso ya mika kansa ga hukumar EFCC bayan kauce wa gayyatar da hukumar ta yi masa a baya

PREMIUM TIMES ta samu labari daga majiya mai tushe cewa hukumar EFCC ta gama shiri tsaf domin a kamo mata tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso kan wasu harkalla da ake zargin sa da aikatawa a lokacin yana gwamnan Kano.

Hukumar ta aika masa da takardar gayyata sau da yawa amma ya ki amsa gayyatar haka wai saboda isa. Daga nan ne majiya ta sanar mana cewa hukumar ta na shirin aikawa da jami’anta su taso mata keyar Kwankwaso sai kwatsam ga kawo kan sa da kansa.

Majiya ta ce Kwankwaso ya isa hukumar EFCC da ranar Asabar da safe.

Wanda ya kai kara ya ce yana zargin Kwankwaso da yin sama da faɗi da nuna son kai ga wasu kuɗaɗen yan fanshon jihar wanda suka rika tarawa cikin kuɗaɗen su wanda gwqmnati ta yi musu alkawarinngina musu gidaje.

Har ila yau wanda ya kai karar ya ce sai bayan an saka hannu akan takardun amicewa da kwangilolin daga baya sai Kwankwaso ya wancakalar da wannan yarjejeniya yayi gaban kansa, maimakon ayi abinda ya kama sai ya rika rabawa ya ƴan uwa da abokan arziki kawai.

Wannan badaƙala an tafka shi ne a watan da Kwankwaso zai sauka daga kujerar mulkin a 2015 wanda mataimakin sa Abdullahi Ganduje a lokacin ya ɗare kujerar gwamnan jihar.