Duk wanda bai yi rigakafin Korona ba, ba zai shiga ginin ma’aikatun gwamnatin Kaduna ba – El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta gargaɗi ma’aikatan jihar da mutane kowa ya garzaya a yi masa rigakafin korona sannan a bashi shaidar yi domin nan da kwanaki 10 idan ba ka da shi ba za aka shiga ofisoshin gwamnatin jihar ba.

A wata sanarwa wanda maiba gwamna El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Talata, gwamnati ta ce ranar Asabar ce ranar ƙarshe da za yadda wa ma’aikaci ko bakon ofisoshin gwamnatin jihar ya shiga ba tare da ya nuna shaidar yin rigakafin cutar ba.

” Tuni ma’aikatar kiwon lafiya ta fara yi wa ma’aikatan jihar kaf ɗin su rigakafin cutar. Wanda a yadda ta tsara za a kammala ranar 31 ga watan Oktoba.

” Haka nan suma baki da za su zo siyara ma’aikatun gwamnatin, sai sun nuna takardar yin rigakafin. Amma kuma saboda karancin sa an umarci duk ƴan jihar su garzaya ma’aikatar kiwon lafiya domin min yin rajista cewa idan maganin ya zo za su kawo kansu ayi musu allurar dole, sannan kuma sai rufe fuska ta takunkumin fuska.

Kwamishinar kiwon lafiya, Amina Baloni ta hori ƴan jihar su garzaya cibiyoyin kiwon lafiya dake kusa da su domin yin rajista.

Dokar dai zai fara aiki ne daga ranar 31 ga Oktoba.