Batun za a riƙa biyan talakawa N5,000 duk wata tatsuniya ce kawai -Shugaban Kwamitin Kuɗaɗe na majalisar Dattawa

An bayyana cewa sanarwar biyan talakawa miliyan 40 naira 5,000 kowanen su, ba zai yiwu cikin shekarar 2022, domin babu wannan batun kwata-kwata a cikin kasafin 2022.

“Abin da na sani a doka shi ne a cikin kasafin 2022, akwai batun za a cire tallafin fetur. Amma babu batun za a riƙa biyan talakawa miliyan 40 naira 5,000 duk wata.

“To ta yaya za a biya su waɗannan kuɗaɗe alhali ba su a cikin kasafin kuɗin 2022?

“Idan za a biya mutum miliyan 40 naira 5,000 a wata, to a shekara za a biya su naira tiriliyan 2.4 kenan fa. A ina za a samu kuɗin.

“Don haka ni dai labarin maganar kawai na ke ji da kuma karantawa a jaridu. Amma ni ji-ta-ji-ta da tatsuniya kawai na ɗauki maganar.”

Hakan Sanata Adeola ya bayyana wa manema labarai a Majalisar Dattawa.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗaɗe, Sanata Afrika Olamilekan ne ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta iya biya kuɗaɗen a cikin shekarar 2022, tunda dai ba a gabatar da kuɗaɗen a cikin kasafin kuɗi na shekara mai zuwa ba.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana cewa za a ware talakawa miliyan 40 domin a riƙa biyan su naira 5,000, don a sauƙaƙa masu ƙuncin rayuwar da za su iya faɗawa, idan an yi wa litar mai ƙarin kuɗi, daga naira 146 zuwa naira 340.

Babban Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya sun gargaɗi Najeriya cewa babu mafita sai dai ƙasar nan ta cire tallafin fetur da na wutar lantarki, yadda za a riƙa shan su da tsada.

Idan aka ce a riƙa biyan talaka miliyan 40 naira 5,000 a kowane wata, to za a riƙa biyan su alawus na naira biliyan 200 kenan.

Wannan adadin kuwa idan aka lissafa na shekara ɗaya, to sun haura adadin kuɗaɗen tallafin da gwamnati ke biya.

Gwamnatin Buhari za ta tsula farashin litar fetur, amma za a rika bai wa talakawa naira 5000 su rage raɗadin ƙuncin rayuwa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta cire kuɗin tallafin man fetur, wanda hakan na nufin za a ƙara kuɗin litar fetur.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a lokacin ƙaddamar da wani shiri na Bankin Duniya a Najeriya.

Sai dai kuma ta ce gwamnatin tarayya za ta zaƙulo mutane miliyan 30 zuwa 40 da su ka fi kowa talauci a kasar nan ta riƙa ba su naira 5,000 kowace Wata, domin rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su iya afkawa a ciki nan gaba idan an ƙara wa fetur farashi.

Ta ce rarar kuɗaɗen da za a riƙa samu ce za a duba sannan a san ko adadin mutum nawa ne za su riƙa amfana da tallafin.

Idan ba a manta ba, Bankin Bada Lamuni na Duniya, IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin mai domin ta ƙara samun kuɗin shiga. Kuma ta rage kashe kuɗaɗe a ayyukan da ba masu muhimmanci ba.

Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin da na kuɗin wutar lantarki a farkon 2022.

Idan Gwamnatin Najeriya ta yi amfani da shawarar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) har ya cire tallafin man fetur da na wutar lantarki a farkon 2022, ‘yan ƙasar nan za su shiga sabuwar shekara cikin halin ƙuncin rayuwar da ta fi ta shekarar 2021 da ake ciki.

Kai tsaye ba wani abu ba ne cire tallafin man fetur da na wutar lantarki, ma’ana ita ce a ƙara wa farashin litar man fetur da wutar lantarki kuɗi.

IMF ta gargaɗi Najeriya cewa yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa idan auna su da waɗanda ta ke samu, to za’a ci gaba da samu wawakeken giɓi a kowace shekara, kamar irin wanda aka samu a bana cikin 2021, to haka ma za ta kasance a shekara mai zuwa.

“Amma idan aka cire tallafin fetur da na kuɗin lantarki, an kamo hanyar saisaita matsalolin ƙaranci kuɗi a hannun gwamnati kenan.

“Amma kuma tilas sai ita gwamnatin ta bijiro wasu tsare-tsaren da za ta rage wa talakawa tsadar rayuwa, sakamakon matsin da za su shiga idan an ƙara kuɗin fetur da kuɗin wutar lantarki. Kuma dama akwai wannan sharaɗin a cikin Sabuwar Dokar Man Fetur ta 2021 cikin watannin baya.”

IMF ya ƙara da cewa, tafiyar-hawainiyar da sabon tsarin canjin kuɗaɗe ke yi, tare da rashin tabbas na kasa maido maƙudan kuɗaɗen da ɓarayin gwamnati su ka sace suka ɓoye a waje, ya rage ƙarfin yawan shigowar jari mai nauyi a Najeriya.”

Wasu ƙarin matsalolin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da fuskanta, a cewar IMF, sun haɗa da ƙarancin kayan da Najeriya ke fitarwa waje.

A kan haka sai IMF ta nemi Najeriya ta fito da wani tsari da zai daɗe tsawon lokaci ya na hana kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje raguwa.