ƘARIN KUƊIN FETUR: Ƙungiyar Ƙwadago ta ci kwalar gwamnati, ta ce an raina talakawa shi ya sa aka yi masu ƙaryar tallafin naira 5,000

Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) ta ce ba za ta taɓa bari gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗin fetur ba, kamar yadda ake ta sanarwa.

Shugaban NLC Ayuba Wabba ne ya fitar da sanarwar a ranar Alhamis, inda ya ce akwai raina wa talakawan Najeriya wayau da hankali a batun ƙarin kuɗin fetur ɗin.

Wabba ya ce NLC na bibiyar batun, inda ya ce kawai gwamnati na so ne ta biya wa Turawan mulkin mallaka buƙatar da su ka nema ta a janye tallafin fetur.

A cikin fushi Wabba ya ce abin da ya fi ban-haushi a batun ƙarin kuɗin man, shi ne romon-kunne da aka yi wa talakawan ƙasar nan, inda aka ce wai za a riƙa ba su naira 5,000 domin su riƙa rage raɗaɗi.

“Ai wannan rainin wayau ne kawai, domin idan ka duba za ka ga kuɗin da za
A riƙa biyan talaka miliyan 40 a shekara ɗaya, sun zarce kuɗaɗen tallafin shekara ɗaya da gwamnati za ta cire.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed da Shugaban NNPC Mele Kyari sun bayyana cewa ƙarin kuɗin zai iya kai lita ɗaya ta fetur naira 320 zuwa 340.

NLC ta ce matsawar aka ƙara kuɗin fetur, to ‘yan Najeriya za su ƙara shiga mawuyacin halin da ya nunka wanda ake ciki yanzu.

“Tsadar rayuwa za ta ƙaru, farashin kayan abinci da kayan masarufi zai tashi sama, sannan kuma matsin rayuwa zai ƙara afka mutane da dama cikin aikata muggan laifukan da matsalar tsaro za ta ƙara muni a ƙasar nan.

A yau ne kuma Shugaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Dattawa, Sanata Adeolu ya ce labarin za a riƙa bayar da naira 5,000 ga talakawa miliyan 40 duk tatsuniya ce, domin babu batun a cikin kasafin 2022.