BARKEWAR CUTAR DIPHTHERIA: Kano ce ke gaba wajen yawan masu fama da cutar, yayin da mutum 836 suka kamu a Najeriya, 80 sun mutu

Najeriya ta samu adadin mutane 836 da aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da 80 suka mutu daga diphtheria tsakanin Mayu da Yuni 2023.

Bisa ga rahoton cutar diphtheria da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta fitar a ranar Asabar, an tabbatar da adadin wadanda suka kamu da cutar a kananan hukumomi 33 a cikin jihohi bakwai da FCT a kasar nan.

Bisa ga sakamakon rohoton bincike da NCDC ta yi nazari a kai, an samu mutum 2,455 da ake zargin sun kamu da cutar daga jihohi 24. Sannan kashi 71.5 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yara kanana ne masu shekaru 2 – 14.

Bisa ga rahoton, jihar Kano ce ke da adadin mutum 819 daga cikin mutum 836 da suka kamu da su.

Jihar Legas ce ta zo ta biyu a jadawalin da aka samu mutane takwas, sai Yobe da Katsina mai uku da biyu.

Jihohin FCT da Osun da Kaduna da kuma Kuros Riba sun samu mutum guda.

Jihohin Kano, Yobe, Katsina, Lagos, FCT, Sokoto, da Zamfara sune ke da kashi 98.0 na wadanda ake zargi.

Gargadin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi kan cewa baba da yaro kowa ya yi ta kan sa, kada ya bari cutar Diphtheria ta kama shi.

Sashen Wayarwa da Gargadi na Ɓangaren Lafiya ya yi wannan gargaɗi a ranar Litinin, ya ce kowa ya yi nesa daga kamuwa da cutar.

Sashen ya ce cuta ce da ke kisa ba tantama, wacce ƙwayoyin halittar cuta ce ke haddasa ta.

Cutar na ɗarsashi a cikin jiki daga kwana biyu zuwa biyar, amma idan ta yi tsawo za ta yi har kwana goma.

“Ya zama wajibi musamman yara kasa da shekaru biyar da dattawa sama da shekaru 60 a kiyaye sosai.”

“Da ma yara waɗanda ba a gama yi masu allurar rigakafi ba, har jama’a su guji cinkoso da ma’amala da ƙazanta.

“Masu yawan fama da rashin lafiya su yi hattara. Masu tafiya a inda cutar ta shiga, a yi hattara. Haka a wurare da ba masu lura da harkokin lafiya.”

Cutar Diphtheria:

Cutar Diphtheria cuta ce da ƙwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ke haddasa ta.

Cutar ta fi saurin kama yara da manya, musamman waɗanda ba su yi allurar rigakafin cututtuka da ake yi wa yara ba.

Cutar kan kama maƙogaro, hanci sannan wasu lokuta har za a farga mutum na yakunewa.

Cutar ya fi yaɗuwa idan ana yawan zama kusa da waɗanda suke ɗauke da ita, idan mai ɗauke da cutar ya riƙa yin tari ko atishawa a tsakanin mutane.

Alamun cutar sun haɗa da zazzabi, majina, ciwon makogoro, idanu su yi jajawur, tari da kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai riƙa ganin wasu farin abubuwa na fitowa a kusa da maƙogaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi.

Hanyoyin Samun Kariya Daga Cutar:

1. Yin allurar rigakafi.

2. Saka takunkumin fuska, musamman idan za a shiga cikin mutane.

3. Toshe baki da hanci idan za a yi tari ko atishawa.

4. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

5. Zuwa asibiti idan aka kamu da zazzaɓi, ko idan ba a gane lafiyar jiki ba.