SHARI’AR HARIN JIRGIN ƘASA: Mai Shari’a ya kori lauyoyi da ‘yan jarida daga shari’ar Tukur Mamu

Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya, a Abuja, ya kori lauyoyi da ‘yan jarida daga zaman sauraren shari’ar zarge-zargen haɗa baki da ‘yan ta’addar da ake yi wa Tukur Mamu.
Zarge-zargen da ake yi masa suna da alaƙa da rawar da ya taka wajen sako wasu da dama waɗanda masu garkuwa su ka riƙe.
A zaman da kotun ta yi ranar, mai gabatar da kara E. A Laswe ya shaida wa kotu cewa ya zo da masu bada shaida. Daga nan ya ce amma kotu ta sallami Lauyoyi da manema labarai.
Za a iya tunawa cewa a zaman da ya gabata, Kotu ta ce za ta rufe fuskokin masu bada shaida kan Tukur Mamu, bayan hana kowa shiga.
Amma ba ta ce za ta haɗa da lauyoyi da manema labarai ta hana su shiga ba.
A zaman baya, Kotun Tarayya ta amince da roƙon da Gwamnatin Tarayya ta yi, ta nemi rufe fuskokin masu bada shaida kan Tukur Mamu, bayan hana kowa shiga.
Za a hana shiga cikin mota Kotun, lokacin da ake bayar da shedakan Mamu.
Ana tuhumar sa da laifin haɗa baki da ‘yan ta’addar da suka yi fashi a cikin jirgin kasa, a cikin 2022.
Mai Shari’alnyag Ekwo ya bayar da damar gabatar da masu shaidar, bayan lauyan Gwamnantin Tarayya, D.E Laswe ya nemi haka.
Abin Da Zai Faru A Zaman Kotu A Ranar:
1. Za a gudanar da zaman shari’ar ba tare da masu kallo ba, sai wasu manema labarai.
2. Za a rufe fuskar masu bada shaida.
3. Kotu ta amince da ba za a bayyana sunayen masu bada shaida ba, za a yi amfani da wasu sunaye daban.
Lauyan Mamu ya ki amincewa, amma Mai Shari’a ya ɗage zaman zuwa 21 ga wata, saboda ba a gabatar da Mamu ba a ranar.
Daga ranar da aka kama Mamu har yanzu ba a bada belin sa ba.