BADAMBADAMAR KWANGILA: Yadda Buhari ya goyi bayan Minista Ameachi a rigimar sa da Gambari kan wata babbar kwangila

Wani rikici mai kama da ‘turnuƙu faɗan ibilisai’, wai yaro bai gani ba balle ya raba, ya ɓarke a Fadar Shugaban Ƙasa, tsakanin Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, Ibrahim Gambari.

Ministan Harkokin Sufuri Ameachi ya zargi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Gambari da yi masa katsalandan a tsarin bayar da kwangila a ma’aikatar sa.

Wannan dai shi ne rikici na baya-bayan nan da ya fito fili tsakanin manyan jami’an gwamnatin Buhari.

Ameachi dai a cikin wani raddi, ya zargi Gambari da yi masa katsalandan a buga tandar zaɓen kamfanoni biyu daga cikin kamfanonin da suka nemi a ba su kwangilar Aikin Sa-ido Kan Manyan Jiragen Ruwa Masu Dakon Kaya (ICTN).

Wannan gagarimin aikin kwangila dai a Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa za a yi shi, wadda ke ƙarƙashin kulawar Minista Amaechi.

Binciken ƙwaƙwaf ɗin da PREMIUM TIMES ta yi, ta gano cewa Shugaba Buhari da Minista Amaechi sun bayar da kwangilar lamari na tsaro a jiragen da tashoshin ga kamfanoni biyu wato MedTech Scientific Limited da Rozi International Limited.

Binciken dai ya nuna Buhari da Amaechi sun karya doka, ƙa’ida da cancantar bayar da kwangilar ga kamfanonin da ba su cancanta ba.

Kenan an karya ƙa’idar da ke shimfiɗe a cikin dokokin Hukumar Tantance Kwangiloli (BPE).

Yayin da Premium Times ta gano cewa MedTech Scientific Limited kamfanin sayar da magunguna ne, shi kuma Rozi International Limited kamfanin hada-hada da duoalncin manyan gidaje ne.

Amaechi ya samu nasarar kauce wa ƙa’idar da BPE gindaya, har ya samu Buhari ya sa masa hannun amincewa kan kwangilar.

Yadda Gambari Ya Rungumi Gidogar Kwangila:

PREMIUM TIMES ta fahimci cewa Gambari ya yi amfani da wasiƙar da BPE ta aika cewa Buhari da Amaechi ba su bi ƙa’idar da ta shimfiɗa ba wajen bada kwangilar, sai ya yi ƙoƙarin a fasa bayar da kwangilar ga kamfanonin biyu.

Cikin wasiƙar da Gambari ya aika wa Ameachi a ranar 14 Ga Oktoba, ya yi ƙoƙarin nuna ƙarfin isar sa a batun kwangilar.

Shi kuma Amaechi ya bayyana hujjar sa cewa kazar-kazar ɗin da Gambari ke yi kan kwangilar, ba ya na yi don kishin ƙasa ba ne, don amfanin kan sa ya ke yi.

Amaechi ya shaida wa Buhari cewa Gambari ya tura wata ‘yar sa mai suna Bilkisu Gambari, ta je wurin sa ta nemi a bata kwangilar.

“Na gano cewa Gambari ya ƙara matsa-ƙaimin sukar bada kwangilar ga kamfanonin biyu tun bayan da ‘yar sa Bilkisu Gambari ta same ni ofis tare da wasu abokan mu’amalar kasuwancin ta, su ka nemi a ba su wannan kwangila ta aikin ICTN.” Haka Amaechi ya bayyana cikin wata wasiƙar da ya aika wa Buhari.

“Na fahimci don a bayar da wani ɓangare na kwangilar ga ‘yar sa Bilkisu ne ya sa Gambari ya bayar da shawarar cewa a karkasa kwangilar a ba kamfanoni da yawa, duk kuwa da yin hakan ya karya ƙa’ida.”

A cikin wasiƙar, Amaechi ya roƙi Shugaba Buhsri ya sa Gambari ya daina yi masa katsalandan.

Premium Times ta tuntuɓi Gambari, amma bai ce komai ba. An an tura masa saƙon tes, har yau bai maido amsa ba.

Wasiƙar Amaechi ta isa teburin Shugaban Ƙasa a ranar 15 Ga Oktoba, 2021, kuma ya amince a ci gaba da bayar da kwangilar ga waɗancan kamfanoni biyu da ya amince da su, duk kuwa da cewa su na da matsalar rashin cancanta, kuma Buhari da Amaechi sun saɓa ƙa’idar bayar da kwangila wadda BPE ta shimfida.

Yadda Buhari Ya Watsa Wa Gambari Ƙasa A Ido:

A wani lamari mai kama da watsa ƙasa a ido, Buhari ya umarci Ibrahim Gambari ya rubuta wa Amaechi wasiƙar sanar da shi cewa Buhari ya karɓi ƙorafin da ya yi Gambari, kuma zai ja masa kunne.

Gambari ya rubuta wa Amaechi wasiƙa inda ya sanar da shi cewa Buhari ya Buhari ya karɓi ƙorafin sa kan shi Gambari ɗin, kuma ya amince wa Amaechi ya bada kwangilar ga waɗancan kamfanoni biyu, MedTech da Rozi.

Kwangila Ko Kiran Sallah Da Garaya?:

A ranar 1 Ga Nuwamba, Premium Times Hausa ta buga labarin yadda Buhari da Amaechi suka gabji kwangilar aikin kula da jiragen ruwa, su ka danƙara wa ‘malaman tsafta da dillalan gidaje’.

Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi sun karya ka’idoji da dokokin sharuɗɗan bayar da kwangila, inda su ka ɗauki kwangilar maƙudan kuɗaɗe ta aikin da ya shafi killace bayanan tsaro a Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, suka bai wa kamfanonin da kwata-kwata ba aikin su ba ne, hanyar jirgi daban, ta mota daban.

Kamfanin da aka bai wa kwangilar dai bai san komai a harkar ayyukan tashoshin jiragen ruwa ba. Aikin kamfanin kawai shi ne kwangilar kayan ayyukan lafiya.

Zai yi kwangilar tare da wani kamfanin haɗin-guiwa, wanda shi kuma aikin sa shi ne dillanci da gina manyan rukunin gidaje kawai.

Tuni dai Hukumar Tsntsncewa da Duba Cancantar Kwangila da Cancantar Ɗan Kwangila (BPP), ta ce wannan lamari da ya faru abin kunya ne da zubar da kuma da mutunci. Sannan kuma ta ce kwangilar haramtacciya ce, amma babu yadda hukumar za ta iya yi, tunda Shugaba Buhari ne da kan sa ya karya ƙa’ida, ya sa hannun amincewar a bai wa kamfanonin da ba su dace kuma ba su cancanta ba kwangilar.

Waɗannan bayanai duk PREMIUM TIMES ce ta bankaɗo su, kamar yadda za ku karanta hujjojin da za a bijiro da su a ƙasa.

Wannan katafariya kuma haramtacciyar kwangila ta jefa manyan jami’an gwamnatin Buhari cikin yanayin jifar juna da habaice-habaicen zargi.

Ita kuwa Hukumar BPP wadda aka karya ƙa’idojin da ta shimfiɗa, aka ɗauki kwangilar aka bai wa kamfanonin da ba a tantance ba, tuni ta rubuta takarda ta rashin jin daɗi, wadda a fakaice kawai takardar wadda PREMIUM TIMES ta gani, ta na nuna cewa Buhari da Amaechi sun karya doka da ƙa’ida, inda su ka ɗauki aikin garambawul ɗin keke su ka bai wa wanda ko ɗaure ƙararrawar keken ma bai iya ba.

Binciken PREMIUM TIMES dai ya dogara ne da wasiƙun da su ka riƙa karakaina, waɗanda ke ɗauke da umarnin Shugaban Ƙasa da umarnin Amaechi da kuma irin martanin da Hukumar BPP ta riƙa maidawa, inda ta ke nuna rashin dacewar da aka nuna, inda aka ƙi bin ƙa’ida.

An Karya Dokar Bada Kwangiloli Ta 2007 -BPP:

Hukumar da ke kula da tantance cancantar adadin farashin kwangila da cancantar kamfanin da za a ba kwangilar, wato Bureau for Public Procurement (BPP), ta ce an karya sharuɗɗa da ƙa’idojin da doka ta gindaya a Dokar Bada Kwangiloli ta 2007.

Aikin kwangilar da ake magana an bayar ɗin dai shi ne aikin yin amfani da na’urorin da ke nunawa ko iya gane duk inda wani jirgin ruwa ɗauke da kaya ya ke (ICTN) idan ya shigo Najeriya da kuma wanda zai fita ko ya fita daga Najeriya.

Wannan aiki ne mai samar da maƙudan kuɗaɗen haraji a ƙasa, idan aka yi shi kamar yadda doka ta tanadar. Sannan kuma aiki ne da ya shafi batutuwan tsaron ƙasa.

Wata wasiƙa da Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta aika wa BPP a ranar 26 Ga Agusta, 2021, ta ce a yanzu za a ci gaba da aikin ICTN, wanda gwamnatin baya ta dakatar.

Yadda Amaechi Da Buhari Suka Ba Mai Tallar Kifi Fiɗar Karsana:

A ranar 11 Ga Satumba, 2020, Ameachi ya rubuta wa BPP wasiƙa ta neman iznin yin wata ‘yan tandar neman aikin kwangiloli ga wasu zaɓaɓɓun kamfanoni domin yin aikin ICTN ga manyan jiragen ruwa masu dakon kaya. PREMIUM TIMES ta ga wannan kwafen wasiƙar.

Ganin yadda a gwamnatin baya wannan aiki ya jawo rikicin da har EFCC ta shiga lamarin, sai BPP ta maida wa Amaechi amsa cewa ba ta yarda a ware wasu zaɓaɓɓun kamfanoni a ce za a yi masu tanda ba. Sai dai a yi bai-ɗaya, irin wadda ƙasashen duniya ciki har da Najeriya su ka amince da ita (ICB).

“BPP ba ta yarda ba. Amma ta yarda a yi tanda ɗin a bisa ƙa’idar da doka da ƙasashen duniya su ka amince. Ta haka za a iya samun kamfanoni waɗanda su ka cancanta daga waje, waɗanda za su iya yin aikin da zai biya buƙata.” Inji amsar BPP ga Amaechi, wadda aka aika masa a ranar 22 Ga Oktoba, 2020.

Amma cikin mamaki a ranar 19 Ga Agusta, 2021, sai Amaechi ya aika wa BPP da sanarwa wadda ke ɗauke da amincewa da sa hannun Shugaba Buhari cewa a bayar da kwangilar kai-tsaye ga MedTech Scientific Limited, wani kamfanin hada-hadar magunguna da kayan asibiti.

MedTech Scientific Limited zai yi aikin ne tare da Rozi International Limited, kamfanin dillancin manyan gidaje da ayyukan gine-gine.

PREMIUM TIMES ta gano cewa babu wasu takardun da da Amaechi ya aika wa BPP domin tabbatar da cewa MedTech Scientific Limited da Rozi International Development Limited sun taɓa ko su na da ƙwarewar ayyukan hada-hadar sa-ido kan manyan jiragen ruwan dakon kaya.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi, ya nuna cewa mai tallar kifi ne aka ba aikin fiɗar karsana kawai.

Dama shi Amaechi karya irin wannan ƙa’ida ba a wannan ce farau ba.