Kotu ta yanke wa barawon kan wata gawa da ya guntile bayan an birne hukunci dauri

A ranar Laraba ne kotun majistare dake Iyaganku ta yanke wa Saheed Olapade mai shekara 32 hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru biyu bayan an kama shi da kwarangwal din kan mutaccen mutum.

Alkalin kotun Patricia Adetuyibi ta ce ta yanke wa Olapade wannan hukunci ne domin ya zama abin koyi ga mutanen dake cin zarafin gawa sannan da gaggawar amsa laifin sa da ya yi.

Lauyan da ta shigar da karar Foloke Ewe ta bayyana cewa ‘yan sanda sun kama Olapade ranar 18 ga watan Nuwamba da karfe 2 na dare a yankin Foko da kan mutum kuma na mace.

“A wannan rana Olapade da abokin sa sun koma inda aka birne wannan mata da ta rasu da rana cikin dare suka hako gawar sannan suka guntile kanta suka saka a jaka.

“Daga nan sai Olapade ya tari dan achaba domin ya kai sa wani wuri inda suna hanya ne ‘yan sanda suka tare su.

Ewe ta ce a hannun ‘yan Olapade bai bada bayanin dalilin da ya sa yake dauke da kan mutum ba sannan abokinsa da suka aikata wannan aiki tare ya arce ba a kama shi har yanzu.

Kotun ta sa a saki dan achaban da ya dauki Olapade saboda ya ce bashi da masaniyar abin dake faruwa.