An kama masu kai wa ƴan bindiga manfetur a dazukan Katsina

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta yi nasarar kama wasu motoci biyar da ke shigar wa ƴa bindiga manfetur ciki daji.

Jami’an sun yi wannan nasarar ne bayan samun bayanan sirri, inda suka yi gaggawar tare su kafin su kai ga inda ƴan ta’addan suke.

  • An kama masu kai wa ƴan bindiga manfetur a dazukan Katsina
  • Ya kamata a ƙara wa Sanatoci albashi a rage kuma yawansu~ Rochas Okorocha

Kakakin Rundinar a jihar Katsina SP Isah Gambo, shi ne ya tabbatar da hakan a madadin Kwamishinan ƴan sandan jihar, Sanusi Buba yayin gabatar da waɗanda ake zargi ga  manema labarai a hedikwatar rundunar ‘yan sandan ranar Litinin.

Katsina Post ta naƙalto SP. Gambo na cewa, rundunar ‘yan sanda ta lura da yadda wasu direbobin ƙananan motoci ke siyan man fetur da yawa, inda ta yi zargin suna kai wa ƴan fashin dajin ne cikin dazuka.

Yayin da ake yi masu tambayoyi, waɗanda ake zargin sun amsa cewa tabbas suna siyar wa ‘yan bindigar man fetur a daji.

An wallafa wannan Labari September 21, 2021 7:15 PM