TAKARAR ZAƁEN 2023: Babu wata hujjar hana miƙa wa ƙabilar Igbo mulkin Najeriya – Rochas Okorocha

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, kuma Sanatan Imo ta Yamma, Rochas Okorocha, ya bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa Jam’iyyar APC ta ƙi damƙa takarar zaɓen shugaban ƙasa a 2023 a hannun yankin Kudu maso Gabas.

Okorocha ya yi wannan furuci ne ranar Litinin a Abuja, a yayin taron ganawa da manema labarai, a Hedikwatar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), a Abuja.

Ya ce tabbas akwai yarjejeniyar da ba rubutacciya ba a APC cewa za a riƙa yin mulkin karɓa-karɓa. Kuma a yanzu lokaci ne da idan dai adalci za a yi, to a yankin Kudu maso Gabas ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya kamata ya fito.”

Rochas ya ce tabbas ana maida ƙabilar Igbo saniyar-ware a wannan gwamnati, amma ba wannan ne abin damuwar ba.

“Magana a yanzu ita ce kowane yanki ya yi shugabanci kuma an ga kamun ludayin su. Don haka a yi adalci a miƙa mulki a hannun ƙabilar Igbo, domin shi ma a ga na sa kamun ludayin.”

Rajin Rochas Okorocha ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Sanata Abdullahi Adamu na Jihar Nasarawa ya ce kada a bi tsarin karɓa-karɓa, a bi cancanta kawai ko ma daga ina a ɗauko ɗan takarar APC.

Sai dai kuma kwata-kwata Rochas bai yarda da ra’ayin sa ba.

“Idan aka ce za a sake fito da ɗan takara daga Arewa, ai kuwa za a samu ɓaraka a APC, domin sauran yankuna za su yi mata kallon jam’iyyar ‘yan Arewa zalla.”

Tuni dai a jam’iyyar APC tafiya ta yi nisa wajen tallata jagoran jam’iyyar, Bola Tinubu.

A gefe ɗaya kuma wata ƙungiyar CPG ta bayyana, mai hanƙoron ganin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya maye gurbin Shugaba Buhari a zaɓen 2023.