Najeriya ba za ta fallasa masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda ba -Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Najeriya ba za ta fallasa masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda ba.

Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na Channels, ranar Litinin a Abuja.

Adesina ya ce maimakon a fito ana fallasa su ko a kunyata ta su, gwamnati ta maida hankali ne wajen tabbatar da cewa an gurfanar da su, an hukunta su.

Adesina na magana ne a kan wasu ‘yan Najeriya shida da ƙasar UAE ta lissafa a cikin jerin mutum 38 da ta ce su na ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda.

“Najeriya ba za ta fallasa su ko ta kunyata su kowa ya gan su ya san su a yanzu ba. Maimakon haka, ta maida hankali ne a kan ganin an hukunta su.

“Kuma tun lokacin da UAE ta fito da bayanin, Ministan Shari’a na Najeriya ya yi magana ya ce za a gaggauta tuhumar su da yanke masu hukunci.

“Saboda haka mai yiwuwa yanzu bincike ya na matakin EFCC. Ko kuma ba mamaki ya na hannun Hukumar Leƙen Asiri ta NIA.” Inji Adesina.

Da aka taɓo masa batun shin ko Buhari zai sake kinkimo bashi a Taron Shugabannin Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, sai Adesina ya ce ai taron ba na neman bashi ba ne.

“Ba taron neman bashi ba ne. Amma dai wasu shugabannin kan keɓe su tattauna hulɗoɗi a tsakanin ƙasashen su. Kuma bashin da Shugaba Buhari ke ciwowa a yanzu ai ana yin ayyukan raya ƙasa ne da su. Saɓanin Gwamnatin baya, wadda idan an ciwo bashin, a cikin aljifan su su ke danna maƙudan kuɗaɗen.” Cewar Adesina.