An Dakatar Da Paul Pogba Daga Wasan Kwallon Kafa Tsawon Shekaru 4

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta bayyana cewar, kotun hukunta laifin shan kwayoyin kara kuzari tsakanin ‘yan wasa ta Italiya ta dakatar da tauraron dan wasan Faransa Paul Pogba daga harkar kwallon kafa tsawon shekaru 4 bayan an tabbatar cewa akwai sinadarin kara kuzari a cikin jininsa.