AMURKA: Kashi 78% na ‘yan Republican Trump su ke so ya sake tsayawa takarar shugaban Amurka a 2024

Yayin da mafi yawan Amurkawa ke ganin cewa kamata ya yi tsohon Shugaban Ƙasa Donald Trump ya daina tunanin sake tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa a 2024, kashi 78% bisa 100% na ‘yan jam’iyyar sa ta Republican da mafi yawan ‘yan Independent na cewa ya fito kawai su sake zaɓen sa.
Haka kuma duk da shari’ar da ya ke fuskanta, duk da cacukui da aka taɓa yi da shi, har yanzu dai a cikin jam’iyyar su ta Republican babu mai farin jinin sa.
Wannan rahoto ya fito ne daga binciken da cibiyar Moris Poll ta gudanar kwanan nan.
“Kashi 78% bisa kashi 100% na ‘yan jam’iyyar Republican da kuma kashi 49% bisa 100% na ‘yan Independent sun ce Donald Trump su ke so ya tsaya masu a zaɓen shugaban ƙasa na Amurka, a cikin 2024.
“Yan jam’iyyar Republican ko gezau ba su yi ba dangane da jafa’in shari’ar da Trump ke fuskanta.
Yayin da zaɓe ke ƙara gabatowa, a kowane mako farin jinin Trump sai ƙara haɓaka yake yi.
Cikin makon jiya kashi 58% bisa 100% ke goyon bayan sa. A cikin wannan makon kuwa adadin yakai kashi 78% bisa 100%.”
A ranar 24 Ga Agusta, Trump ya kai kan sa kurkuku a Yankin Fulton, a Jihar Georgia, Kudu maso Gabacin Amurka.
Ya yi sarandar miƙa kan sa kurkuku, bisa zarge-zarge 13 da ake yi masa, ciki har da zargin shirya hayagagar sauya sakamakon zaɓen 2020 na Jihar Georgia.
Wannan shi ne karo na huɗu a cikin 2023 da Trump ya fuskanci tuhumar aikata laifuka.
Ana cajin sa tare da wasu mutane 18. Amma ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
Har yanzu dai bakwai daga cikin 18 ɗin da ake zargi tare da Trump sun ƙi kai kan su ga hukuma, har zuwa ƙarshen ranar Alhamis.
Amma an ba su wa’adin kai kan su ga hukuma zuwa ranar yau Juma’a, 12 na rana agogon Amurka, na EST.