RUGUJEWAR GININ ABUJA: Da rabon ina da sauran zama a duniya, domin ina shiga ginin ya rufta da mu

Akalla mutum biyu ne suka mutu a sanadiyyar ruftawar wani bene mai hawa biyu a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ginin wanda a ciki akwai shaguna da gidajen zama dake layin Legos a Garki ya rufta da misalin karfe 11 na daren Laraba, a lokacin da mafi yawan mutanen dake kwana a ciki sun kwanta.
Aminu Idris wanda mazaunin wannan bene ne ya ce ginin ya rufta a lokacin da yake kokarin ya shiga ɗakin sa ya kwanta.
“Ina shiga ginin tare da kanne na sai ginin ya rufta da mu. ‘yan uwa na sun mutu kuma mutane da dama sun ji rauni.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA FEMA duk da du aka yi aiki ceto mutanen da ginin ya rufta da su.
Jami’ar hulda da jama’a na hukumar FEMA Nkechi Isa ta bayyana cewa hukumar ta ceto mutum 37 babu abin da ya same su, ba su ji rauni sannan da wasu mutum biyu da suka ji rauni.
Nkechi ta ce hukumar tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda za su ci gaba da bincike domin ceto sauran mutane.