Aisha Matawalle ta rabawa mata audugar tsafta, ta ce suna buƙatar kula ta musamman a yayin al’ada

Uwar gidan Gwamnan Zamfara ta shirya taron wayar da kan yara mata ɗalibai a makarantar Sakandaren mata ta Samaru dake Gusau a wani sashe na bikin ranar tsaftar mata ta duniya.

Ƙungiyar sa kai ta ‘WASH United’ ta ƙasar Jamuce ta samar da wannan rana ta tsaftar mata a shekarar 2013 domin sanar da murya ɗaya wurin neman ɗaukan matakai tare da wayar da kai da kai kan lamuran tsafta da lafiyar mata a duniya a yayin da suke al’ada.
Da take magana a wurin taron, Matar Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Aisha Muhammad Bello Matawalle wadda ta samu wakilcin Hajiya Fatima Musa, mai baiwa Gwamna shawara, ta ce taron na daga cikin ƙoƙarin uwar gidan gwamna na goyon baya da tallafawa mata da ilimi kan tsaftar su tare da tabbatar da cewa kowace ƴa mace ta yi al’ada cikin tsafta da koshin lafiya ba tare da tsangwama ko kunaya ba.
Ta ƙara da cewa, taken ranar na wannan shekara shi ne “Mataki da zuba jari a tsaftar mata da lafiya” inda ta nemi da a ilmantar da ƴaƴa mata  tare da zayyano mafita ga matsalolin dake damun mata manya da yara a faɗin duniya a ta dalilin al’ada.
Matar gwamnan ta nemi al’umma sun haɗa ƙarfi da ƙarfe a  wurin kawo ƙarshe a wannan fanni wanda yake tasiri wurin kawo cikas ga karatun mata, lafiyar su.
Ita ma a yayin da take gabatar da lacca a taron, babbar ma’aikaciyar jinya a ofishin matar gwamna Larai Ka’oje, ta yi wa ɗaliban ƙarin haske kan inganta tsafta a yayin al’ada domin kaucewa kamuwa da cututtuka da za su iya kaiwa ga samun matsala a lokacin haihuwa.
A cewarta, kula da tsaftar kai a yayin al’ada na da muhimmanci ga lafiya, ƙwarin jiki da haihuwar mata.
A yayin jawabin rufe taron, shugabar makarantar Hajiya Kulu Shehu ta yi godiya ga matar gwamna bisa zabar makarantar mata ta Samaru domin yin bikin wannan rana ta wannan shekara tare da tallafawa ɗalibai da audugar tsafta da wayar da kansu kan lafiya.