Naira 500 ta koma dala 1 a kasuwar ‘yan canji

Alƙawarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kafin ya hau mulkin ƙasar nan, cewa zai maida darajar naira daidai da darajar dalar Amurka, ya na neman zama tatsuniya, ganin yadda a ranar Talata ɗin nan farashin dala ɗaya a kasuwar ‘yan canji ta kai har naira 500.

PREMIUM TIMES ta leƙa wani rumbum da ake tattara farashin kuɗaɗen waje a kasuwar ‘yan canji, rumbun da ake kira abokiFX.com inda ta ga sabon farashin dala ɗaya ya kai naira 500 a kasuwar ‘yan canji.

Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Babban Bankin Najeriya CBN, ya karya darajar naira a idon kuɗaɗen ƙasashen waje, wurin azarbabin karbo bashin dala biliyan 1.5 a waje.

Babban Bankin Najeriya CBN, ya karya darajar naira a ranar Litinin, inda farashin dala gwamnatance ya tashi daga naira 379 zuwa naira 410.25.

CBN ya buga wannan sabon farashi a shafin sa na Twitter, a ranar Litinin, inda ya kankare rubutaccen farashin naira 379 duk dala daya, ya maye gurbin sa da sabon farashin dala daya a kan naira 410.25.

Hakan na nufin CBN ya karya darajar naira, inda darajar ta ya ragu da kashi 7.6%.

A yanzu CBN ya dora farashin dala kan farashin ‘Nafex’, wato farashin da ake bai wa masu shigowa Najeriya su zuba jari da kuma masu fitar da kaya daga Najeriya zuwa wasu kasashe, kan naira 410.25.

Cikin watan Maris Gwamnatin Shugaba Buhari ta karyata zargin ta karya darajar naira, lokacin da Ministar Kudi Zainab Ahmed ta bayyana amfani da tsarin ‘Nafex’.

Sai Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa naira 379 ke farashin gwamnati, naira 410 kuma farshin farashin wasu hada-hadar musamman na gwamnati.

Kafin karya darajar naira dai a ranar Litinin, ta na da farashi uku da su ka hada da Farashin CBN na dala 1 naira 379. Akwai Farashin Nafex naira 410.25 duk dala 1. Sai kuma Farashin Kasuwar Tsaye, wato ‘Yan Canji, ita kuma naira 486 duk dala 1.

CBN ta hade farashin ne wuri daya domin Najeriya samu sararin amincewa a ba ta lamunin dala biliyan 1.5.

A makon da ya gabata dai naira 486 ake sayar da dala ɗaya, amma a yau har ta kai naira 500.