Aƙalla Yara ƙanana sama da 1,000 ne suka kamu da cutar bakon dauro daga Janairu zuwa Maris a jihar Sokoto

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Sokoto Ali Inname ya bayyan cewa aƙalla yara sama da 1,000 ne suka kamu da cutar bakon dauro daga watan Janairu zuwa Maris 2022 a jihar.

Ali ya ce cutar ta barke a kananan hukumomi 23 dake jihar.

Yayin da yake yin kirar karfafa gwiwa ga iyaye na s rika bari ana yi wa ƴaƴan su allurar rigakafin cututtukan dake kashe yara ya ce mafi yawan yaran da suka kamu da cutar yara ne da ba su yi allurar rigakafi ba.

“Mun samu yaran da suka yi allurar rigakafi da suka kamu da cutar amma koda suka kamu din cutar bai kwantar da su ba kamar yadda ya yi wa wadanda ba su yi rigakafin ba.

Ali ya ce cutar ta kashe wasu yara a kauyukan Dan Madi, Kaurare da Aljannare dake karamar hukumar Tambuwal.

Ya ce gwamnati ta bude wuraren yi wa yara allurar rigakafi 500 a fadin jihar Amma har yanzu akwai iyayen dake hana bada ‘ya’yan su domin yi musu allurar rigakafi.

Duk da haka kwamishinan ya ce gwamnati ta aika da jami’an lafiya domin gudanar da bincike a wuraren da suka fi fama da yaduwar cutar.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa jihar Sokoto na cikin jihohi 8 da suka fi fama da yaduwar bakon dauro a kasar nan.

Hukumar ta kuma ce jihar Sokoto na cikin jihohin da ba sa yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi.

Asusun UNICEF ta bayyana cewa kashi daya bisa 10 na yara a jihar ne kawai ake yi wa allurar rigakafi.

A jihar yara kashi 78% daga cikin yara 1,000 ke mutuwa duk shekara.

Domin dakile yaduwar cutar gwamnati a shekarar 2017 ta tsara shirin yi wa yara miliyan daya allurar rigakafi a jihar sai dai bisa ga adadin yawan yaran da suka kamu da cutar a bana ya nuna cewa gwamnati ba ta iya cimma burin ta.