GARKUWA DA FASINJOJIN JIRGIN ƘASA: Gwamnati na ƙoƙarin ganin an ceto waɗanda aka kama -Lai Mohammed

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta na yin dukkan ƙoƙarin da ya dace wajen ganin ta ceto dandazon fasinjojin jiragen da aka yi garkuwa da su a dajin Kaduna, ciki watan Maris.
Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana wa manema labarai haka a Faɗar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, a ranar Laraba.
Mohammed ya ce duk da dai ba zai bayyana wa ‘yan jarida takamaiman irin ƙoƙarin da ake yi ba, “amma dai ina tabbatar ma ku da cewa a yanzu ɗin nan da mu ke magana, ɓangaren gwamnati daban-daban na can na yin ƙoƙarin ganin an ceto mutanen da ran su da lafiyar su.”
Minista Lai Mohammed ya ƙara da cewa “abin da gwamnatin tarayya ke yi ba abu ba ne da za a fito a wurin taron manema labarai ana yayata shi ba.
Ya ce musamman saboda akwai butun rayuwar waɗanda ake tsare da su, kada lamarin ya dagule masu.
“Amma dai ɓangarorin jami’a tsaro da dama na aiki ba dare, ba rana domin bin-diddigin yadda harin da garkuwar su ka faru domin lalubo yadda za a ceto su da ran su da lafiyar su.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka kai wa jirgin hari a ranar 28 Ga Maris, bayan jirgin ya bar Abuja, kan hanyar sa ta zuwa Kaduna, tsakanin Katari.
Aƙalla mutum 8 aka bada rahoton mutuwar su.