Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata a jihar Zamfara

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata da ba a san adadin yawan su ba a kwalejin kiwon lafiya da ke Tsafe jihar Zamfara.
Tsafe na daya daga cikin garuruwan dake fama da hare-haren ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Wata majiya a garin ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bindigan sun kai hari rukunin gidajen daliban wajen karfe 11:24 na daren Talata sannan suka yi garkuwa da dalibai mata dake zama a gidan.
Dama dai wannan gidan haya ne wanda ɗalibai ke zama a cikin su.
Yayan ɗaya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su Asamau Salisu, Usman Abdullahi, ya ce sun tashi da safen Laraba ne da labarin cewa an yi garkuwa da ‘yar uwar su.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya tabbatar yin garkuwa da daliban kwalejin ranar Laraba da safe.
Shehu ya ce ‘yan bindigan sun afka wani gidan haya da karfe 3 na safiyar Laraba suka yi garkuwa da mata hudu.
“Tabbas kamar yadda wasu gidajen jaridu suka buga ‘yan bindigan sun kai hari wani gidan haya dake kusa da kwalejin da dalibai ke zama inda suka yi garkuwa da mata biyar sai dai daya daga cikin su ta gudu ta dawo gida.
Shehu ya tabbatar cewa rundunar ta aika da jami’an ta domin ceto daliban da ƴan bindigan suka tafi da su.