Ƙananan ƴan kasuwa 600 sun amfana da tallafin miliyan sha-biyar a Gusau da Tsafe

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe Hon. Kabiru Ahmadu (Mai Palace) ya ƙaddamar da raba tallafin kuɗi naira miliyan N15,000,000 ga ƙananan ƴan kasuwa a mazabarsa.

An ƙaddamar da raba tallafin ne ga ƙananan ƴan kasuwa da manoman rani.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Bungudu ya kubuta daga hannun ƴan bindiga
Ƙananan ƴan kasuwa 600 sun amfana da tallafin miliyan sha-biyar a Gusau da Tsafe

Rukunin farko da aka ƙaddamar da shirin da su wanda ya ƙunshi mutum ɗari biyu, sun karbi horo daga masana akan yadda za su yi amfani da waɗannan kuɗi a cikin kasuwancinsu da kuma nomansu na rani don ganin sun samu albarka a cikin abinda suka samu.
Bayan kammala bada horon ne wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar asusun ‘Nigerian Lottery Trust Fund’ aka raba wa waɗanda suka samu horon naira N25,000 ga kowannen su.
A cewar ɗan majalisan, sauran mutane ɗari huɗu da za aka raba su zuwa rukuni na biyu da na uku za su karbi nasu horon tare da tallafin kuɗin a ranar Lahadi da Litinin.

Tura Wa Abokai

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaNITDA ta horar da mata Ƴan Jarida kan Fasahar Sadarwar Zamani

Labari na gabaDa Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Bungudu ya kubuta daga hannun ƴan bindiga

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.