Laifin da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna ya yi wa sarki Sanusi II – Daga Binta Tsafe

Mohammed Abdullahi wanda aka fi sani da ‘Dattijo’ ya yi suna suna a jihar Kaduna da ya kai ga saboda kusancin sa da gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya sa ake masa ganin shine zai tsayar ɗan takarar gwamnan jihar a 2023.

A jihar Kaduna, ana yi wa Dattijo ganin shine mafi kusanta da gwamnan jihar.

Bayan zaben 2019, El-Rufai ya naɗa shi shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar domin ya daɗa jawo shi a jika da kusanto shi kusa da gwamnati

Sai dai kuma kwale-kwalen sa ya ci karo da gingimemen dutse.

A duniya kowa ya san cewa gwamna El-Rufai ba shi da wani aboki na kud-da-kud da ya wuce Sarki Muhammadu Sanusi II. Idan ba don asali ba za ka iya kiran su tagwaye.

Duk inda ka ga El-Rufai za ka ga Sarki Sanusi. Shakuwar su da zumuntar su ba tun yanzu ba saboda haka ne ma karkashin mulkin El-Rufai a jihar Kaduna, Sarki Sanusi ya ke tare da gwamnan a ko da yaushe.

El-Rufai da Sarki Sanusi sai Allah.

Kuskuren ‘Dattijo’

Tun bayan tsige shi daga sarautar Kano da gwamna Abdullahi Ganduje yayi Sarki Sanusi ya ci gaba da gudanar da al’amurorin sa na yau da kullum kamar yadda ya saba.

A kullum cikin mulki da sarauta ya ke, kuma ana daraja shi a Najeriya kamar sarkin da ke kan kujerar mulki a jihar.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Kaduna, Mohammed Abdullahi, ‘Dattijo’ ya tafka kuskuren kiran sarkin Kano Sanusi a matsayin tsohon Sarki a wajen taro a Kaduna. Wannan kuskure da yayi ya yi matukar ɓata wa sarki Sanusi rai inda a lokacin da ya zo yin jawabin sa sai ya fara da yi wa Abdullahi ‘Dattijo’ albishir.

” Ka yi kuskure babba, kira na da ka yi tsohon sarki, babu abu kamar haka. Amma kai ma zan kira ka da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, amma ba za ka gane ba sai nan gaba kaɗan.

Bayan sarki Sanusi ya kammala jawabin sa ya tafi ya zauna sai Abdullahi ya yi maza-maza ya je ya tsuguna domin ya nemi gafarar laifin da yai masa. Amma kuma bakin Alkalami ya bushe.

Jim kaɗan bayan wasu kwanaki sai gwamna El-Rufai ya sanar da sauye-sauye a gwamnatin sa ciki har da sauya wa Abdullahi wurin aiki, ya cire shi daga ofishin gwamna zuwa kwamishinan kasafin kudi na jihar.

Masu yin sharhi na cewa rashin sani shine ya jefa Abdullahi cikin wannan tsautsayi. Suna ganin da tun farko an koya masa yadda zai kira sarki Sanusi da da bai tafka wannan kuskure ba.

Mohammed Abdullahi ‘Dattijo’ matashi ne mai kwazon gaske wanda ake ganin yanazu a jihar Kaduna musamman waɗanda ke makusantan gwamnan jihar, Nasir El-Rufai babu kamar sa. Dattijo mutum ne mai saukin kai sannan matashi da ya san darajar mutane kuma ɗan gidan sarauta. Abinda yayi ba ganganci bane ko kuma da gangar. Idan da zaka tara ƴan Najeriya Miliyan miliyan ɗin kaf haka za su yi wa sarki Sanusi laƙabi da, ‘ Tsohon Sarkin Kano’ domin ba za su san ba haka ake masa laƙabi da ba. Ya na da matuƙar wuya ace kowa ya san yadda za a yi wa sarkin laƙabi da musamman a wannan zamani da ake ciki na wayewa. Shima tsautsayi ne kuma kamar yadda sarki Sanusi ya yi misshi albishir ɗin zama tsohon shugaban ma’aikata, ya tabbata haka.

Allah ya huci zuciyar sarki Sanusi.