Akwai alamomin saisaitar matsalolin Arewa maso Gabas -Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ta bayyana cewa akwai alamomin samun sauƙi da rangwame a matsalolin ta’addancin da ya dabaibaye Yankin Arewa maso Gabas, inda rikicin ta’addancin Boko Haram ta shafe shekaru sama da goma ya na kassarawa.

Mataimakin Babban Sakataren Ma’ajiyar Ɗinkin Duniya, Ahunna Eziakonwa ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Juma’a.

Ya yi bayanin ne ganin irin ci gaban da ake ta samu wajen daƙile matsalar ta’addanci da ‘yan ta’adda a yankin, musamman a Jihar Barno.

Madam Eziakonwa, wadda kuma ita ce Daraktar Shiyyar Afrika ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ƙara da cewa sa hannun da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi a lamarin ya taimaka ƙwarai wajen samun gagarimin ci gaba.

Jami’ar wadda ta ce ta zo Najeriya ne domin yin nazarin irin tasirin da tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi a yankin wanda ke fama da kashe-kashe fiye da shekaru goma, ta ce duk da ana samun ci gaba, har yanzu akwai ɗimbin ayyukan da su ka zama wajibi a taimaka domin cim masu.

Ta ce ta kawo ziyara a Najeriya cike da alhini da karsashi a zuciyar ta, kasancewa a Najeriya aka haife ta, kuma a Najeriya ta yi wayau.

“Don haka dawowa a nan na yi wannan aiki abin karkashi ne a zuci matuƙa, domin a nan na fara aikin taimakon agaji tare da gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya, domin taimaka wa waɗanda wannan masifaffen bala’in rikici ya shafa.

“Ina farin cikin sanarwa cewa, lokacin da mu ka fara wannan aiki shekaru biyu da su ka gabata, ba mu ma san ko za mu iya samun nasara, ko ba za mu iya samun nasara ba. Saboda matsalar rikicin. Amma abin farin ciki sai ɗimbin masu bayar da gudummawa da tallafi su ka gaskata mu.”

Ta ce har yanzu akwai sauran aiki, amma ƙoƙarin da ake kan yi ya nuna akwai alamun shawo kan lamarin baki ɗaya.

Ta ziyarci wasu yankuna da ke kan iyaka dà Kamaru, inda ta tsallaka kan iyaka da ƙafa.

Ta ce a wasu wurare harkoki sun dawo kamar da.

Ta ce an sake buɗe makarantu, malamai na ci gaba da koyarwa, kuma dama haka UN ta tsara kenan.

Ta ce babban dalilin tashe-tashen hankulan yankin Arewa maso Gabas shi ne rashin bada gaskiya ga gwamnati a ɓangaren talakawa.

Ta ce dalili kenan duk ƙarairayin da Boko Haram ke wa matasa, sai su riƙe shi da hannu bibbiyu.