Kimiyya Da Fasaha: NITDA ta horar da mata Ƴan Jarida a Jigawa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa NITDA ta horar da mata ‘yan jarida 50 da aka zabo daga jihohin Arewa maso Yamma kan aikin jarida na zamani kuma ta raba musu kwamfutoci 50 da nufin zamanar musu da aikin su.

Taron bitar na kwana biyu da aka gudanar a 3 Star Hotel da ke Dutse, fadar jihar Jigawa, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Mata Ƴan Jarida ta Ƙasa, reshen jihar Jigawa, ya samu halartan Darakta Janar na hukumar NITDA, Malam Kashif Inuwa Abdullahi wanda hadimin sa, Bashir Ibrahim ya wakilta.

Kimiyya Da Fasaha: NITDA ta horar da mata Ƴan Jarida a Jigawa
Ana zargin ƴar aiki da sace sarƙoƙin gwal da darajar su ta kai miliyan goma a Kaduna

Da yake buɗe taron bitar, Bashir Ibrahim ya bayyana cewa, manufar horon ita ce wayar da kan ƴan jaridan kan Fasahar Sadarwa (ICT) a aikin jarida tare da zamanantar da aikin musamman ga mata.
A jawabinta na buɗe taron, Shugabar Ƙungiyar Mata Ƴan Jarida ta Najeriya reshen jihar Jigawa Hauwa Ladan, ta yaba da kokarin Malam Kashif Inuwa Abdullahi.

Tura Wa Abokai

Raarraba

Facebook

Twitter

Labarin bayaAna zargin ƴar aiki da sace sarƙoƙin gwal da darajar su ta kai miliyan goma a Kaduna

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.