Gwamnatin ta fitar da mutum miliyan 4.2 daga ƙangin fatara cikin shekaru biyu – Ministan Gona

Ministan Harkokin Noma da Bunƙasa Karkara, Mohammed Abubakar, ya bayyana cewa an fitar da mutum miliyan 4.2 daga cikin ƙangin talauci a fannin noma, a cikin shekaru biyu.

Ministan ya yi wannan iƙirarin ne ranar Juma’a a Abuja, a lokacin da ya ke jawabi Ranar Abinci ta Duniya (World Food Day).

“A ƙoƙarin mu na tabbatar da an samu wadatar abinci, an samar da ruwa a wurare 446, inda aƙalla gidajen yankunan karkara 286,500 ke amfana.

“Kuma mun wadatar da kayan hasken lantarki 11,952, tare da taransafoma biyar mai ƙarfin 500KVA a yankunan karkara, domin bunƙasa ayyukan samar da abinci.

“Ta hanyar bijiro da tsare-tsaren ƙarfafa manoma da jari ko tallafi da sauran hanyoyi, mun ceto aƙalla mutum miliyan 4,205,576 daga ƙuncin rayuwar fatara da talauci a cikin shekaru biyu.

“Za a ci gaba da fitar da mutane daga fatara da talauci a fannin noma, domin hakan na cikin alƙawarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa a cikin shekaru 10 zai fitar da mutum miliyan 100 daga fatara da talauci.

“An tabbatar cewa fannin noma ne kaɗai ya samu bunƙasa a ƙasar nan a lokacin annobar korona. Har ya taimaka wa ƙasa da kashi 24.23 na bunƙasar tattalin arzikin cikin gida GDP).” Inji ministan.

Sai dai kuma Minista Abubakar ya nuna damuwa a kan ƙalubalen matsalar tsaro da ke damun harkokin noma a Arewa.

Ya ce wannan matsalar ta kawo cikas ga samun wadataccen kayan abinci ga manoman karkara, tsawon shekaru uku a jere.

Ya yi ƙorafin matsalar rikicin Fulani makiyaya da manoma, mahara, ɓarayin shanu da masu garkuwa da mutane, ya ce duk sun kawo wa harkar noma cikas.

Ya ce ya na da yaƙinin cewa tsarin samar wa makiyaya gandun kiwo na ƙasa da aka fito da shi, zai magance matsalolin, sannan ya samar da wadataccen nama kuma lafiyayye a ƙasar nan.