Shan miyar kuka da miyar ayayo na samar da muhimman kariya ga lafiyar jiki – Likita

Wani likita dake koyar da darasin ‘Biochemistry’ a jami’ar Ilorin jihar Kwara Olamilekan Bello ya yi kira ga mutane da su maida hankali wajen shan miyar kuka ko miyar ayoyo domin samun kariya daga wasu muhimman kwayoyin cututtuka.

Bello ya kara da cewa akwai wasu kwayoyin cuta da wutar dake fita daga wayoyi da na’urori masu kwakwalwa suke yi wa jikin mutum

Ga amfanin da miyan kula yake da shi a jikin mutum.

1. Ganyen kuka na dauke da sinadarin Vitamin C wanda ke taimakawa wajen karfafa garkuwar jiki ta hanyar kare mutum daga kamuwa da wasu cututtuka kamar mura da saurin warkar da rauni a jiki.

2. Ya na dauke da sinadarin calcium Wanda ke taimakawa wajen karfafa kashi.

3. Miyan kuka na kara jini a jiki saboda akwai sinadarin Iron a ciki.

4. Yana maganin ciwon typhoid, da zazzabin cizon sauro.

5. Yana taimakawa wajen tsayar da amai da gudawa.

6. Ganyen kuka na rage zafin radadin ciwon hakori.

7. Yana rage kiba a jiki.

8. Miyan kuka na taimakawa wajen inganta lafiyar masu fama da ciwon siga.

Amfanin miyan ayoyo.

1. Yana taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da ciwon siga.

2. Ayoyo na dauke da sinadarin Protein wanda ke taimakawa wajen inganta garkuwar jiki.

3. Miyan ayoyo na kare mutum daga kamuwa da ciwon ido da cututtukan Ido da ake kamuwa da su idan an tsufa saboda akwai sinadarin Vitamin B6.

4. Yana Samar wa mutum kariya daga kamuwa da mura.

5. Miyan ayoyo na taimakawa wajen rage kiba a jiki.

6. Ayoyo na saurin narkar da abinci a cikin mutum.

7. Yana taimakawa wajen samar da barci mai nauyi.

8. Ayoyo na kara kyan fara.

9. Yana Hana warin baki da hana a kamu da cututtukan dake kama hakora.

10. Yana dauke da sinadarin calcium Wanda Kara karfin kashi.