BINCIKEN ‘Pandora Papers’: Gwamnan da ya sayi gidan da Tinubu ya yi jiyya a Landan ya ce bai aikata laifi ba, amma…

A ƙoƙarin sa na kare kan sa daga labarin fallasa da bankaɗa na Pandora Papers da PREMIUM TIMES ta buga a kan sa, Gwamna Adegboyega Oyetola na Jihar Osun ya bayyana cewa bai aikata laifin komai ba dangane da gidan da aka ce ya saya, inda ya yi amfani da wani kamfanin sa na sirri da ke ƙasashen waje, wato Global Investments Offshore Ltd., ya sayi danƙareren gida a Landan.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamna Oyetola, mai suna Ismail Omipidan ya fitar a ranar Litinin, gwamnan ya ce ai tuni ya cire hannun sa daga kasancewa ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin tun ranar da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya naɗa shi Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Osun, cikin 2011.

Sai dai kuma tulin bayanan takardun da PREMIUM TIMES ta ci karo da su dangane da kamfanin da kuma harƙallar sayen gidan, ba su nuna Oyetola ya cire hannun sa a matsayin ɗaya daga cikin daraktocin kamfanin, kafin ya sayi gidan ba.

Haka nan kuma a cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na sa, Isma’il Omipidan ya fitar, Gwamna Oyetola bai nuna kwafe-kwafen takardun da su ka tabbatar da hujjar sa ta cire sunan sa daga kamfanin, tun cikin 2011 ba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Buhari ya ziyarci Tinubu a Landan, inda ya ke zaune cikin danƙareren gidan da Gwamna Oyetola ya saya daga alhaji gidan ya na hannun kotun Najeriya, ana shari’ar ƙwace shi.

Cikin watan Yuli, Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar cewa Buhari zai tafi Landan domin halartar taro. Sanarwar ta ƙara da cewa kuma Buhari idan ya je, zai tsaya ganin likitocin sa, “domin ƙara duba lafiyar sa.”

A Landan ɗin, an yi gamo-da-katarin haɗuwa da juna tsakanin Buhari da jigon APC, Bola Tinubu.

Tinubu a lokacin shi ma ya na zaman jiyya ne ta wata rashin lafiyar da ba a bayyana ko wace iri ba ce.

Shafukan jagororin biyu na soshiyal midiya sun cika duniya da hotunan Buhari da Tinubu su na zaune a cikin nishaɗi su na taɗi a falon wani ƙasautaccen gida. An kuma nuno wani hoton su a tsaye kowa ɗaure da takunkumin korona a bakin sa.

Bashir Ahmed, ɗaya daga cikin hadiman Buhari a kafafen yaɗa labarai, ya rubuta cewa, “Shugaba Muhammadu Buhari a wannan yammaci ya ziyarci Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.” Ya kai ziyarar ce a ranar 12 Ga Agusta.

Ba a ranar ce su ka fara haɗuwa ba, amma sakin hotunan ya fusata ‘yan Najeriya, saboda a lokacin da su ke a Landan ɗin ganin likitocin su, nan a Najeriya kuma likitoci na yajin aiki.

Abin da ‘yan Najeriya ba su sani ba, shi ne wancan gida inda Buhari ya gana da Tinubu, gida ne wanda ke ɗaya daga cikin gidajen da ɓarayin gwamnantin Najeriya ke saye da kuɗin sata a birnin Landan.

Wannan harƙallar dai ita ce mafi girma da ake fallasawa daga cikin manyan harƙalloli tun bayan hawan mulkin Buhari a 2015.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi ya tabbatar da cewa katafaren gidan da Buhari ya je ya ziyarci Tinubu a ciki, an saye shi ne a cikin kuɗin harƙallar satar wasu biliyoyin nairori, wadda ake shari’a a Najeriya har Gwamnantin Buhari ta samo umarni daga Babbar Kotun Tarayya cewa a ƙwace gidan.

Wanda ya fara mallakar gidan dai wani gogarman ɗan Najeriya ne da ya tsare, amma ya gudu, kuma ya rigaya ya sayar da gidan arha takyaf ga Gwamnan Osun Gboyega Oyetola.

Shi kuma Oyetola ɗan’uwan Bola Tinubu ne na jini.

Wannan harƙalla na ɗaya daga cikin dubban harƙallolin da gamayyar gogaggun ‘yan jarudu na duniya su ka bankaɗo, ciki kuwa har da ‘yan PREMIUM TIMES a ƙarƙashin binciken bankaɗo manyan ɓarayi mai suna Pandora Papers.

Gida Mai Lamba 32, Grove End Road, Landan, shi ne gidan da ake magana. Kuma shi ne Buhari ya kai wa Tinubu ziyara a ciki.

Wannan gida da ke unguwar manyan attajirai a Westminster, Landan ta kasance tamkar dandazon wurin ziyarar ‘yan Najeriya, saboda yawan karakainar da su ke yi wurin budiyar jagoran APC Bola Tinubu a gidan.

Gwamnoni da Sanatoci da ‘Yan Majalisun Tarayya birjik duk sun kai ziyara gidan.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila duk sun je dubiya su ma.

Gidan dai gidan alfarma ne irin wanda talakawan Najeriya sai dai su gani a hoto, ko bai wa filawa ruwa da shara ba su kai matsayin a dauke su aiki a ciki ba.

Gwamna Oyetola ya sayi gidan dala miliyan 8.5 Saboda a rajistar da aka yi wa gidan ta cikin Yuli 2013 mai lamba 340992, darajar gidan na fam miliyan 11.95, kamar yadda aka saye shi a ƙarƙashin Zavlil Holdings Ltd, wanda ke ƙarƙashin kamfanin mai na Shell a Tsibirin British Virgin Islands.

PREMIUM TIMES ta bankaɗo cewa Kolawole Aluko, gogarman da Nejeriya ke nema ruwa jallo, shi ke da kamfanin Zavlil Holdings Ltd., wanda ya fara sayen gidan fam miliyan 11.95

Shi kuma Kolawole Aluko, gogarman ɗan ƙaƙudubar da ya riƙa haɗa baki da tsohuwar ministar fetur Diezani ce su ka saci bilyoyin daloli.