‘Yan sandan Katsina sun damke wasu mata dake yin shigar matafiya suna kai wa ‘yan bindiga fetur a daji

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Gambo Isa ya bayyana wasu mata a bainar manema labarai a rundunar da aka kama suna badda kama a matsayin matafiya suna kai wa ‘yan bindiga mai a cikin daji.

Gambo isa da yake nuna wadanna mata ya ce ana kama su da jakkuna makil kamar da kayan saka wa ashe ba haka bane.

” Ko da muka kama su a iyakar jibiya mun tilasta su su bude jakkuna a ga abinda ke cikin su. Da suka bude sai muka ga man fetur ne daure a cikin zannuwa kamar kayan sakawa za su kai wa yan bindiga.

Isah ya ce gaba dayan su mazauna kwatas din malali ne dake cikin garin Katsina kuma ‘yan sanda sun gano cewa kusan duk unguwar ma sana’ar su kenan saida wa ‘yan bindiga man fetur, kuma mata ne ke yi harda masu shekaru masu yawa.

” Matan sun ce sukan aika yan acaba ne su siyo man a gidan mai. Idan suka cika tankin baburan su sai sukawo musu su kuma su jujjuye a jarkuna. daga bisani kuma sai su daddauresu a ledoji su saka a jakkuna su yi kamar matafiayn gaske ashe munafukai ne.

A karshe Gambo Isah ya ce za a ci gaba da bincike akai domin gano sauran wadanda ke yi wa ‘yan bindiga harkalla.