Yadda hasalallu su ka yi wa gogarman IPOB rugu-rugu da ruwan duwatsu, yayin da ya ke ƙoƙarin tilasta wa jama’a zaman gida dole

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo sun bayyana yadda hasalallu su ka jefe wani tsageren IPOB da tulin duwatsu, bayan ya yi ƙoƙarin tirsasa masu dokar hana su fita gida.

Mutumin dai an tabbatar ɗaya ne daga cikin Dakarun Tsaro na ESN da ke ƙarƙashin IPOB, ya kuma ci dukan tsiya, inda aka rufe shi da duka har sai da aka kashe shi.

Kafin ‘yan sanda su isa wurin ya mutu, kuma su ma abokan ta’asar sa, tserewa su ka yi, yayin da su ka ga hasalallu sun rufe abokin ta’asar ta su da jifa da duka.

‘Yan Sanda sun tabbatar da kashe mutumin mai suna Obinwanne Iwu, ɗan asalin ƙauyen Ahiara a Ƙaramar Hukumar Ahiazu Mbaise a Jihar Imo.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Imo Mike Abattam ya bayyana yadda lamarin ya faru.

“Dama shi Obinwanne Iwu mai shekaru 34, gudajjen ɗaurarre ne a Kurkukun Owerri. To ya ja ayarin ‘yan dabar sa ya shiga kasuwa da niyyar korar jama’a kowa ya koma gida ya zauna, kamar yadda tsagerun IPOB ke cewa kada a fita.

“Sun riƙa ihu da ƙarfi a cikin kasuwa, su na cewa “yau fa Litinin, don haka kowa ya kwace kayan sa, a rufe kantina a koma gida tilas a zauna.”

CSP Abattam ya ci gaba da jawabin sa cewa, “mutanen kasuwar sun harzuƙa, sai su ka cukumi Iwu aka yi cacukui da shi. Aka ɗaure hannayen sa ta baya, su ka riƙa dukan sa har sai da ya mutu. Wasu kuma da su ka ga an fara dukan sa, sai su ka gudu.”

Ya ce har yanzu dai ba a kama kowa ba tukunna.