An kama mutum uku cikin maharan da suka sace daliban makarantar Bethel a Kaduna

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya bayyana cewa rundunar ta kama mutum uku daga cikin mutum 25 da suka yi garkuwa da daliban makarantar Bethel dake Maraban Damishi, Kujama a karmar hukumar Chikun jihar Kaduna.

Mba ya ce rundunar ta kama wadannan mutane tare da wasu ‘yan ta’adda 50 a fadin kasar nan.

‘Yan sanda sun kama Ishaku Lawal, Mu’azu Abubakar da Adam Bello wanda duk suna cikin wadanda ake zargi sun sace daliban makarantar Bethel a Kaduna.

“Yan sanda sun gano cewa Mu’azu Abubakar wanda aka fi sani da Datti mai shekara 27 shine ya je ya duba makarantar sannan ya tsara yadda suka shiga suka kwashe dalibai 131.

“Ishaku Lawal ya ce sun samu makaman da suka yi aiki da su daga wajen wani Ahmadu wanda aka fi sani da Yellow.

“Rundunar ta kama masu maharan da bindigogi kirar AK47 guda uku.

Mba ya kara da cewa wadannan yan bindigan na da hannu a fashi da makami da aka rika yi a yankin.

Idan ba a manta ba a cikin wannan makon shugaban kungiyar kiristocin Najeriya ya sanar cewa mahara sun saki karin yan makaranta 10 cikin wadanda suka rage a hannun su.

Har yanzu akwai mutum 21 da ba a sako su ba.