2023: Tun ina matashi na fara sana’ar siyar da manja a Maiduguri, kasuwanci ba bako na bane -Uzor Kalu

Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Uzor Kalu, ya bayyana yadda ya fara sana’a da yadda ya zama biloniya tun ma kafin a kafa PDP.

A tattaunawar da ya yi da gidan talbijin na ARISE TV mallakar Thisday a ranar Alhamis, Kalu ya ce ya fara kasuwanci da sana’ar sayar da man ja, tun ya na ɗalibin jami’a a Maiduguri.

“Lokacin da ina Jami’ar Maiduguri, sai na fahimci sana’ar man ja na da tasiri a garin sosai. Saboda ana buƙatar sa, amma babu manyan dilolin sa.

“To idan na tafi gida hutu, sai na lodo man ja mai yawa na kawo Maiduguri na sayar ga manyan ‘yan kasuwar man ja.”

Kalu wanda shi ne Bulalar Majalisar Dattawa, ya ce daga nan ya yi sana’ar sayar da kifi. Da ya zama attajiri ne kuma ya koma hada-hadar ɗanyen mai, sugar, kuma ya zama babban dilan sayar wa Sojojin Najeriya makamai. Kalu ya riƙa kai wa sojoji kayan abinci a bakin daga.

A cikin tattaunawar, ya bada labarin cewa ya haɗu da tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida da Buhari tun zamanin mulkin soja, sannan su na manyan hafsoshi. Amma bai bayyana irin yadda su ka taimaka wa rayuwar sa ba.

Kalu shi ne mai jaridun The SUN da Telegraph.

Da Ruben Abati ya yi masa tambaya kan ɗaure shi da aka taɓa yi akan shari’ar zargin satar naira biliyan 7.65, Kalu ya ce wannan duk sharri ne magauta su ka ƙulla masa domin ganin bayan sa.

“Kai Ruben ka san ni sarai tun ma cikin 1992. Tun kafin na zama gwamna ni ƙasaitaccen attajiri ne wanda ya fi ƙarfi ya saci naira biliyan 7.65, har sunan sa ya ɓaci a ce masa ɓarawo.

“Da mulkin siyasa ya dawo, ni na bai wa PDP zunzurutun kuɗi Naira miliyan 500 a farkon kafa ta. Da Obasanjo ya fito daga kurkuku kuma ni na fara ba shi kuɗi masu yawa. Naira miliyan 100 na ɗauka na ba shi.” Haka Kalu ya taɓa faɗa a wata hira da jaridar Guardian ta taɓa yi da shi cikin 2019.

Kalu ya ce bai yiwuwa a ce shi da ya fara kashe wa PDP kuɗi tun farkon kafa ta zamanin mulkin soja, sannan don ya zama gwamna ya ɓuge da satar naira biliyan 7.65.

Ya ce masu jin haushin ya zama ƙasaitaccen attajiri ne tun ya na matashin sa.

A cikin hirar, ya bada labarin cewa har haɗa ƙwanjin takarar shigo da sugar ya yi shi da Ɗangote.

Ranar Talata ce wannan jarida ta buga labarin Kalu na cewa zai fito takarar shugaban ƙasa, idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara.

NAN ta ruwaito Kalu na cewa ƙungiyoyi da dama sun nemi Kalu ya fito takarar shugabancin ƙasa, kuma sun bayyana cewa a shirye su ke domin su tabbatar cewa ya yi nasara a zaɓen 2023.

Sannan kuma an ga fastocin Kalu na neman takara an manna a kan titinan jihohin ƙasar nan da dama.