Da Buhari bai zama shugaban Kasa ba da kila babu Najeriya yanzu – Kalu

Tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu ya zargi gwamnonin Najeriya da bari har matsalar tsaro ya kai matsayin da ya ke yanzu.

Kalu a tattaunawa da yayi da Arise TV ya ce gwamnoni ne suka fi kusa da mutane, sun san masu aikata ta’addanci a jihohin su.

” Idan gwamnoni za su mike tsaye su yaki matsalar tsaroa johohin su su mike, domin shugaba Muhammadu Buhari ya yi iya kokarin sa.

” Bihari ba zai zo jihohin su ya yi musu yaki da ƴan ta’adda ba, sune za su mike tsayi su tabbatar sun yake su.

Kalu ya kara da cewa gwamnoni da yawa ba su takarawar gani ba wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihohin su, ” kowa Buhari amma kuma sune suka fi kusa da waɗannan ƴan ta’addan amma kuma ba su yin komai a kai.

” Gwamnati Buhari ta taka rawar gani matuka, abin da ya ke faruwa a kasarnan a mulkin baya, da Buhari ba zo ba da kila tuni an manta da anyi wata kasa wai Najeriya.

” Wannan shine gaskiyar magana. Amma kuma ya zu ya zage damtse ya tambayar an kawo karshen matsaloli da dama musamman a fannin matsalar tsaron ƙasar nan.

A karshe Kalu ya ce matsalar ƴannbindigavda suka addabi mutane a Najeriya matsalace da ke neman a kashe kuɗi ma su yawa kuma gwamnati na kokarin haka.

Jihohin Arewacin Najeriya na fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga da sace sacen mutane.

A cikin wannan mako mahara sun sace wasu ƴan kasuwa cike da bas bas har hudu a hanyar Birnin Gwari.