Kamfanin NLNG zai kwararo iskar gas wa ƴan Najeriya don karya farashin sa a kasuwa

Sanin kowa ne musamman masu amfani da Iskar gas wajen yin girke-girke cewa iskar ta yi tashin gwaron zabi da ya gagara magidanta da dama a kasar nan.

Mutane da dama sun hakura da siyar iskar has din domin yin girki sun koma amfani da itace da gawayi.

Tukunyar Iskar gas mai nauyin kilogiram 12.5 ya kai har sama da naira 10,000 a kasuwa kafin yanzu.

A dalilin haka, hukumar NLNG ta fidd wata sanarwa rabar Juma’a cewa nan ba da dadewa ba za ta wadatar da ƴan Najeriya da iskar gas wanda zai larya farashin iskar a kasuwa yanzu.

Takardar wanda jami”in hulɗa da jama’a na Kamfanin NLNG Andy Odey ya saka wa hannu ya ce rahe tsadar farashin iskar gas ɗin zai taimaka waje rage raɗadin wahalar tsadan sa a kasuwa.

Shugaban kamfanin mai na kasa Mele Kyari ya yi ƙarin bayani akai inda ya bayyana cewa babbar hanyar da kamfanin ta ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar tsadar farashin man shin a wadata kasar da da iskar gas ɗin ya kai ko ina.

” Hakan zai sa da karfin tsiya farashin ya karye mutane su samu sauki.