2023: Dalilin da ya sa ba a jin rugugin rundunar yaƙin Atiku a Ribas -Gwamna Wike

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya bayyana dalilin da ya sa ba a ganin hotunan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a jerin ‘yan takarar muƙamai na PDP a Jihar Ribas.
Wike ya ce saboda Atiku ya tattago wasu mutane daga jihar ya saka cikin rundunar kamfen ɗin sa, ba tare da tuntuɓar shi Wike ɗin ba.
“Wasu mutane na yawan tambaya ta me ya sa ba a ganin hotunan Atiku Abubakar da na Shugaban PDP a faɗin Jihar Ribas. Ni kuma na kan ce masu to me ku ke nufi ne?
“Ɗan takarar shugaban ƙasa ya shigo jiha ta Ribas, ya ɗauki mutanen da saka cikin rundunar kamfen ɗin sa, ba tare da Gwamna ɗungurugum ya bayar da ta sa gudummawar sunayen ba.
“To kun ga hakan ya nuna ba su so kenan mu taya su kamfen. Saboda haka za mu yi wa waɗanda ke so mu yi masu kamfen ne kawai, kamar ‘yan takarar sanata da ɗan takarar gwamna. Saboda haka mun zo ne nan wurin don mu yi masu kamfen.”
A ranar Litinin ce Gwamna Wike ya yi wannan furucin wurin buɗe Hedikwatar Kamfen ta PDP a Fatakwal
“Sun ce ba su buƙatar ‘yan jihar Ribas su taya su kamfen, to za ku tura kan ku ku shiga ne ba a gayyace ku ba?
“A’a, mu ma babu ruwan mu da su”, haka dandazon jama’a su ka amsa wa Wike.
‘Abokan Gabar Jihar Ribas’
Wike ya ce Atiku ya yi sammakon bubuƙuwa, ya tattago masu gaba da Jihar Ribas ya saka cikin rundunar kamfen ɗin sa.
“Ni ban taɓa ganin inda aka wulaƙanta Jihar Ribas ba kamar wannan lokacin. An je an tattago waɗanda ba su ƙaunar Jihar Ribas ba tare da neman gudummawar mu ko shawara daga gare mu ba.”
Sai dai kuma Wike bai ambaci sunayen waɗanda ya kira masu gaba da Jihar Ribas ɗin ba, ko kuma waɗanda ba su ƙaunar jihar.
Amma dai tsohon shugaban PDP na ƙasa kuma ɗan jihar Ribas, Uche Secondus ne Atiku ya naɗa mashawarcin sa yayin kamfen.