Gwamnatin Buhari za ta yi wa masu rike da mukaman siyasa karin albashi

Hukumar tarawa da rarraba kudin haraji ta kasa ta ce ta kammala shiri sake duba albashin masu rike da mukaman siyasa, da ma’aikatan shari’a, domin dacewa da halin da kasar ke ciki.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce a yanzu ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la’akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za su sake duba albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, kama daga shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, da gwamnoni da kwamishinoni, da kuma albashin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma ‘yan majalisun jiha da na tarayya.

Mista Mbam ya ce hakkin hukumar ne ta tsara albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, tun daga matakin kananan hukumomi da zuwa matakin tarayya, BBC ta ruwaito.

Shugaba Buhari da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai Gbajabiamila yayin gabatar da kasafin kudin 2023.

Haka kuma sanarwa ta ce aikin hukumar ya shafi zababbu da masu rike da mukaman siyasa, ban da albashin sauran ma’aikatan gwamnati, wanda hukumar ta ce ke hannun ma’aikatar tsara albashi ta kasa.

To sai dai kungiyar kwadago ta kasa NLC ta nuna rashin jin dadinta game da matakin, tana mai cewa babu wadanda suka fi cancantar karin albashi a kasar kamar ma’aikatan gwamnati.

Daga dukkan alamu wannan matakin bai yi wa ‘yan Najweiya dadi ba domin tun can albashin ma’aikata na daga cikin abubuwan da suke haifar da cece-ku-ce a Najeriya.

Bayanai na cewa yanzu haka akwai jihohi da dama a Najeriya waɗanda ba su fara aiwatar da tsarin biyan mafi ƙarancin albashi na naira dubu 30 ba ga ma’aikatansu.