Kotu ta ƙwatar wa Gwamnatin Tarayya maka-makan gidajen Diezani a Abuja

A ranar Litinin ɗin nan ce Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar da umarnin kammala ƙwace maka-makan gidaje na biliyoyin nairori, waɗanda tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Diezani Allison-Madueke ta mallaka a Abuja.
Gidajen waɗanda kotun Babban Mai Shari’a Mobolaji Olajuwon ta ƙwace, sun haɗa da katafaren gida mai Lamba 1854, kan Titin Mohammed Mahashir, da ke Aso Drive.
An ƙiyasta gidan zai kai Dala miliyan 2,674,418.
Sai kuma gida mai Lamba 6 da ke Aso Drive a Asokoro, wanda tafkeken gidan alfarma ne na gani na faɗa, wanda Hukumar EFCC ta ce ya kai darajar dala miliyan 380.
Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Awujeran ne ya sanar da ƙwace gidajen a yau Litinin, cikin wata wasiƙa da ya aika wa kafafen watsa labarai.
Baya ga gidajen da aka ƙwace, Awujeran ya ce an kuma ƙwace wasu rabtsatstsun motocin ta biyu, ciki har da wata BMW, wadda aka ƙiyasta kuɗin ta zai kai Naira miliyan 36.
Idan ba a manta ba, EFCC ce ta nemi kotu ta ƙwace kadarorin tun a ranar 29 Ga Nuwamba, 2021.
A cikin watan Janairu 2022, kotu ta umarci EFCC ta buga cewa an ƙwace gidajen domin ana zargin na sata. “Amma idan akwai mai hujjar cewa gidajen sa ne, to ya je kotu da hujjoji.”
Ganin shiru babu wanda ya kai kan sa kotu domin iƙirarin cewa ba da kuɗin sata aka sayi gidajen ba, har wa’adin da kotu ta bayar ya cika, an ƙwace gidajen da motocin a ranar Laraba, 6 Ga Afrilu, 2022.
A yau Litinin ce kotun ta tabbatar da kammala ƙwace kadarorin.
Diezani dai har yau ta na zaune Ingila, tun bayan saukar gwamnatin Goodluck Jonathan cikin 2015.