Ƴan sanda sun kama matashin da ya kashe Ɗan shekara 13 a Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama Auwalu Abdulrashid wanda aka fi sanin sa da Lauje wanda ake zargin sa da laifin yin garkuwa da kashe wata ‘yar shekara 13.

Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a garin Kano a farkon wannan mako.

Kiyawa ya ce bayan wannan ‘Fitsararre’ wanda sunan gayun sa wai ‘Lauje’ ya yi garkuwa da yarinyar ya kashe ta ya kuma birne ta a jikin wani kangon gini.

” Bayan haka kuma sai ya kira iyayenta su biya kudin fansa naira miliyan 1.

Kiyawa ya ce rundunar ta samu wannan labarin ne bayan mahaifin yarinyar ya kawo kara a ofishinsu.

“Mahaifin yarinyar mazaunin garin Tofa dake karamar hukumar Tofa ya ce wanda ya yi garkuwa da ƴarsa ya bukaci a biya shi Naira miliyan 1 amma bayan roko ya amince da Naira 400,000.

Ya ce a dalilin gudanar da bincike da ‘yan sandan suka yi sun gano gawar yarinyar da ya birne kuma sun kama Lauje.

Kiyawa ya ce Lauje na tsare a ofishinsu kuma da zarar sun kammala bincike za su kai shi kotu domin yanke masa hukunci.

” Da yake hannun ‘yan sandan Lauje ya shaida wa jami’an tsaron cewa ya yi garkuwa da dan shekara uku kuma kanin yarinyar da ya kashe inda bayan ya karbi Naira 100,000 ya ajiye yaron a makarantar firamaren Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa.