Gwamnatin jihar Bauchi za ta ɗauki likitoci sama da 1000 aiki a jihar

Shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar Bauchi Yahuza Haruna ya bayyana cewa gwamnati za ta dauki dalibai likitoci 1,061 aiki.

Haruna ya fadi haka ne a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Laraba.

Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin inganta fannin kiwon lafiya da inganta karfin ma’aikata a jihar.

Haruna ya ce za a tabbatar da matsayin kowani likita kafin a bashi wasikar daukan aikinsa.

Bayan haka shugaban ma’aikatan gwamnati ya ce gwamnati za ta dauki dalibai wadanda suka kammala karatu a fannin kula da dabbobi domin basu aikin yi a ma’aikatar noma.

Haruna ya ce yin haka na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin samar wa matasa aikin yi a jihar.

Ya hori daliban da za a ɗauka aiki da su rike amana a aikin da za a basu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa ɗaliban da gwamnati za ta bai wa aiki dalibai ne daga makarantun horas da ma’aikatan jinya da Unguwar zoma da kwalejin koyar da kiwon lafiya da fasaha dake jihar da suke aiki ba tare da ana biyan su albashin ba.