Gwamnatin Buhari ta sakar wa masu amfani da Tiwita mara, amma ta gindiya sharuɗɗa

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage dokar kulle shafin sada zumunta na soshiyal midiya na Tiwita, wanda ta kulle tun cikin watan Yuni, 2021.
An kulle tiwita tare da hana shafin amfani a Najeriya, bayan an buga wani bayani da gwamnatin Buhari ta yi wa kallon tinzara jama’a ne domin su yi wa gwamnati bore.
Sannan kuma Gwamnantin Najeriya ta zargi masu tiwita da ɗaukar nauyin zanga-zangar #EndSARS, wadda ta rikiɗe zuwa mummunar tarzoma a yawancin manyan garuruwan kudancin Najeriya.
Babban Daraktan Hukumar NITDA, Kashifu Abdullahi ne ya yi sanarwar ɗage takunkumin da aka ƙaƙaba wa tiwita har tsawon watanni shida.
Kashifu dai ya kasance da shi aka riƙa jidalin tattaunawar sasantawa tsakanin gwamnatin tarayya da Tiwita.
“Gwamnatin Tarayya ta umarce ni da na sanar da ɗaukacin ‘yan Najeriya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗage takunkumin da ya ƙaƙaba wa Tiwita a Najeriya. Daga yau Alhamis 13 Ga Janairu, 2022 da ƙarfe 12 na safiya ne za a ci gaba da amfani da Tiwita a Najeriya.
“An amince da ɗage dokar bayan Ministan Sadarwar FasaharZamani, Isa Pantami ya aika masa da wasiƙa.