Ƴan Bindiga sun yi awun gaba da Ƴan kasuwan Kano a dajin Birnin Gwari

Wasu da ake zargin mahara ne a yau Labara sunyi awun gaba da wasu Yan kasuwa akan hanyarsu ta zuwa Kano a Dajin Birnin Gwari dake Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a dai dai dajin Unguwar Yako wanda yayi ƙaurin suna wajen satar mutane a hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari, inji Wanda abin ya faru akan idonsa amma ya nemi a sakaye sunansa.

Muna tafiya ne cikin jerin gwanon motoci da rakiyar sojoji amma wadanda sukayi gaba su aka tare aka nausa dasu daji, muna kallo ana tafiya dasu, inji direban.

Munzu mun tarar da motoci kusan guda hudu amma babu kowa a cikinsu. Sojojin sunbi sawon barayin kuma daga baya sun kirawo Jirgin Sama yana shawagi a inda barayin suka bi, inji deriban.

Muhammad Jalige, Kakakin Yan Sandar Jihar Kaduna bai dauki wayar da akayi masa domin jin ta bakin hukumomin Yan Sanda.