Ƴan bindiga sun durfafi Kano, sun fasa ɗaki sun ɗauke mahaifiyar Dan Majalisa a Gezawa

Wasu ‘yan bindiga sun ritsa mahaifiyar Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dokokin Kano, Isyaku Ali, su ka arce da ita.

Lamarin ya faru a Gezawa, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke iyaka da birnin Kano.

Ɗan sa Sani Ali ne ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa maharan sun dira gidan ta wajen ƙarfe 1 na dare, suka kutsa gidan su na neman a nuna masu ɗakin da mahaifiyar ɗan majalisar ta ta ke kwance.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Honorabul Ali ya shaida wa jaridar cewa maharan sun karya ƙofar ɗakin gyatumar, su ka kutsa da ƙarfin tsiya, su ka fito da ita.

“Har zuwa yanzu dai ba su kira lambar kowa ba, ballantana a ji halin da ta ke ciki.

“Amma dai ina addu’a a duk inda ta ke, Allah ya tsare ta.” Inji shi.

Tuni mahara sun fara addabar yankunan Kano da kewayen jihar.

Ba kuma wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari a Gezawa ba, duk kuwa da cewa garin ya kusa haɗewa da Kano.

Cikin 2021 ne aka shiga har garin aka yi garkuwa da wani attajiri.